Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta lallasa Liverpool da ci 4-0 a wasan da ta karbi bakuncin Liverpool din a filin wasa na Etihad.
Wannan na zuwa ne mako daya bayan Liverpool ta lashe gasar Frimiya karo na farko cikin shekara 30 bayan da Chelsea ta doke Man City din mai biye mata a matsayi na biyu.
Dan wasan tsakiya na kungiyar ta Man City, Kevin De Bruyne ne ya jefa kwallon farko a ragar Liverpool a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Daga bisani Raheem Sterling da Phil Foden suka jefa kwallaye na biyu da na uku kafin hutun rabin lokaci.
Dan wasan Liverpool Oxlade Chamberlain ya shigo wasan da kafar hagu inda ya ci kansu da kwallo ta hudu da ta kawo wa Liverpool rashin nasara mafi girma a kakar bana a gasar ta Frimiya.