✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool ta gasa wa Aston Villa aya a hannu

Salah ya zama na farko da ya ci kwallo ko ya bayar aka zura a raga a wasa 10 a jere a Firimiya.

Liverpool ta gasa wa Aston Villa aya a hannu yayin da ci ta 3-0 a wasan mako na huɗu a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Anfield.

Sabon ɗan kwallon da Liverpool ta ɗauka Dominik Szoboszlai ne ya fara ci mata ƙwallo a minti na uku da take leda, sannan Matty Cash na Villa ya ci gida.

Liverpool ta ƙara na uku ta hannun Mohamed Salah, bayan da suka koma zagaye na biyu a karawar.

Salah ya zama na farko da ya ci kwallo ko ya bayar aka zura a raga a wasa 10 a jere a Premier League tun bayan bajintar da ya yi tsakanin Agusta zuwa Disambar 2021 da ya yi karawa 15 a jere.

Liverpool, wadda ta yi canjaras ɗaya da cin wasa uku a jere za ta je gidan Wolverhampton ranar 16 ga watan Satumba a wasan mako na biyar a Premier.

Ita kuwa Aston Villa, wadda ta ci wasa biyu aka doke ta karawa biyu za ta karɓi baƙuncin Crystal Palace a dai ranar 16 ga watan na Satumba.