✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Litinin za a sanar da Gwarzon dan kwallon Duniya

A ranar Litinin 11 ga watan nan da muke ciki ne ake sa ran za a sanar da wanda ya lashe Gwarzon dan kwallon duniya…

A ranar Litinin 11 ga watan nan da muke ciki ne ake sa ran za a sanar da wanda ya lashe Gwarzon dan kwallon duniya na shekarar 2015 a wani bikin karrama ’yan kwallo da hukumar kwallon kafa ta duniya  FIFA za ta yi a Hedkwatarta da ke Zurich na Swizilan.
’Yan kwallo uku ne za su fafata a gasar da suka hada da Lionel Messi da Neymar na FC Barcelona da ke Sifen da kuma Cristiano Ronaldo na kulob din Real Madrid da ke Sifen. Tuni ’yan kwallo  da masu horarwa da shugabannin wadansu gidajen jaridu da kyaftin-kyaftin na kungiyoyin kwallon kafa a kasashen duniya ne suka kada kuri’unsu wajen zabo gwarzon dan kwallon.  Abin da ya rage shi ne sanar da sakamakon zaben a ranar Litinin a wajen bikin karramawar. Sannan a ranar ce za a bayar da kyaututtuka ga bangarori daban-daban a harkar kwallo.
Cristiano Ronaldo ne yake rike da kambun bayan ya lashe sau biyu a jere kuma sau uku a tarihin gasar, yayin da Lionel Messi ne ya fi kowane dan kwallo yawan lashe gasar inda ya lashe har sau hudu idan kuma ya samu nasarar lashe ta ranar Litinin zai kasance ya lashe sau biyar kenan a tarihin gasar.  Shi kuwa Neyram bai taba lashe gasar ba, hasalima wannan shi ne karo na farko da ya shiga sahun wadanda za su fafata a matakin karshe na gasar.
Lionel Messi ya kai wannan matsayi ne bayan ya zura kwallaye 48 daga wasanni 56 da ya yi wa kulob din FC Barcelona. a kakar wasa ta 2015.  Kuma ya taimaka wajen zura kwallaye 24 (Assists) a raga.  Ronaldo kuma ya zura kwallaye 48 ne daga cikin wasanni 52 da ya buga wa kulob din Madrid a shekarar 2015.  Sannan ya taimaka wajen zura kwallaye 14 (assists) a raga.  Shi kuma Neymar ya zama na uku ne a jerin wadanda za su fafata bayan ya zura wa FC Barcelona kwallaye 45 a raga daga cikin wasanni 59 da ya yi a shekarar 2015.  Sannan ya taimaka wajen zura kwallaye 13 (assists) a raga.
 Shahararrun ’yan kwallo irin su Ronaldinho da Del Piero da Andiy Shebchenko da Carlos Puyol da sauransu tuni suka kada kuri’unsu amma sai a ranar Litinin ce za a sanar da wanda ya lashe gasar.
Masana harkar kwallo sun yi hasashen Messi ne zai lashe gasar a karo na biyar bayan ya taimaki kulob din FC Barcelona wajen lashe kofuna biyar a kakar wasan da ta wuce yayin da Ronaldo kuma bai lashe wani kofi a kakar wasa ta 2015 ba in ban da yawan kwallayen da ya zura a raga.