✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lissafi ya fi kowane darasi sauki – Malamin jami’a

Ya ce akasarin dalibai kan tsani Lissafi ne saboda yadda ake koyar da su.

Wani malamin Jami’a mai kwarewa a bangaren Lissafi, Dokta Ohi Uwaheren ya ce darasin ya fi kowanne sauki a dukkan darussan da ake koyarwa a makarantu.

Malamin, wanda yake koyarwa a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara ya ce akasarin dalibai kan tsani Lissafi ne saboda yadda malamansu suke koyar da su.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da wata makala a bikin yaye dalibai da kaddamar da mujalla wacce makarantar Brilliant Stars International School ta shirya ranar Litinin a Ilorin.

A cewar malamin, sabanin yadda ake tunanin darasin a daya daga cikin masu wahala, a zahirin gaskiya Lissafi na daya daga cikin darussan da suka fi kowanne sauki a makaranta.

Ya ce, “Lissafi ba shi da wahalar da mutane da dama ke tunanin yana da ita.

“Idan malaman da ke koyar da dalibai Lissafi za su canza salon koyarwarsu, labarin zai canza sosai.

“Ya kamata mu rika saukaka darasin ne ba wai mu rika firgita dalibai da shi ba.

“Idan malami ya shiga aji kamar za shi yaki, dole dalibai su firgita, daga nan kuma su ji sun tsani darasin,” inji shi.

Daga nan sai malamin ya shawarci malaman da su rika nuna kwarewa wajen sauke nauyinsu na koyarwa, musamman ga yara kanana.

Ya ce koyar da yara wata muhimmiyar dama ce ga malamai ta kafa wani harsashi a zukatansu wanda zai yi matukar wahala a goge shi.

Daga cikin kwararrun hanyoyin koyarwa a cewarsa, dole ne malami ya saita koyarwarsa daidai da fahimta da kuma tunanin daliban, muddin yana so su fahimta.