✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Limami ya maka jikansa a kotu kan kwace masa mata

Dattijon ya neman kotu ta hukunta jikan nasa kan aikata kwartanci.

Wani limamin coci ya maka jikansa a kotu bisa zargin jikan nasa da kwace masa mata da kuma da.

Fasto Sale Ekah mai shekara 73 ya shaida wa Babbar Kotun Yanki da ke Makurdi a Jihar Binuwai cewa jikansa ya kwace masa mata mai juna biyu ya hada da sauran matansa, har sai da ta haifi da namiji.

“Jikana, wanda ake zargi ya kwace mini mata. A da can tallan koko take zuwa kuma duk lokacin da ta kawo tana kawo min kullin koko in saya.

“Daga baya iyayenta suka amince ta rika zuwa tana taimaka min da yin girkin, da haka har ta fara sha’awar in aure ta.

“Na nuna mata cewa na yi mata tsufa, saboda tana da kuruciyarta, amma ta nace har sai da na aure ta,” kamar yadda ya shaida wa kotun.

Limamcin cocin, ya shaida wa kotun a ranar Alhamis cewa ya auri matar tasa ne bisa al’adar kabilar Idoma kuma ya cika duk sharuddan auren.

Ya kara da cewa jikan nasa da ya kwace masa mata a 2017, shi ma dan kabilar Idoma ne, kuma tanade-tanaden dokar al’adar kabilar za su yi cikakken aiki a kansa.

A cewarsa, hukuncin kwartanci, wanda babban laifi ne karkashin Sashe na 387 na kundin manyan laifukan al’adun kabilar Idoma ya hau kan jikan nasa, wanda ke zaune a garin Obagaji na Karamar Hukumar Jihar Agatu ta Jihar.

Bayan sauraron karar, alkalin kotun, Mis Rose Ioryshe, ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 6 ga Satumba, 2021 domin yi wa wanda ake tuhuman tambayoyi.