Kungiyar Likitocin Najeriya (NARD) ta ba wa Gwamnatin Tarayya wa’adin ranar 17 ga watan Agusta ta cika alkawarin da ta yi mats ko likitocin su tsunduma yakin aiki.
Bayan taron Kwamitin Zartarwar kungiyar, ta ce ta kara wa gwamnatin lokacin da ta bayar da mako uku ta magance matsalar karancin albashin likitocin jihohi da rashin biyan alawus na hadarin da ke tattare da aikinsu.
“Idan ba a magance wadannan matsaloli ba, to kungiyar ba ta da zabi face shiga yajin aiki daga ranar Litinin 17 ga watan Agusta, 2020”, inji takardar bayan taron.
Shugaban NARD Dakta Sokomba Aliyu, da Kwamitin Zartarwar kungiyar na neman gwamnati ta samar wa likitocin da ke kula da masu cutar coronavirus isassun kayan kariya, kuma ta biya su alawus da aka ware musu kamar yadda doka ta shar’anta.
Sauran bukatun sun hada da daukar nauyin likitoci su karo ilimi da kuma biyan likitocin jihohi bambancin da ke tsakanin albashinsu da na takwarorinsu da ke aiki a Gwamnatin Tarayya.
“Nan take a biya bashin cikon sabon albashin likitocin da sauran ma’aikatan lafiya”, inji takardar bayan taron.
Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tarayya su yi cikakken bincike a kan rashin biyan hakkokin likitocin da suka rasu a bakin aiki ga magadansu.
“Sannan a biya cikakken diyya ga ‘yan kungiyar da ke aiki a jihohi”, kuma a yi wa ma’aikatan lafiya inshorar rayuwa, inji shugabannin kungiyar.
Sai kuma batun biyan likitoci wadataccen albashi kamar yadda aka yi musu alkawari.
Sun kuma bukaci Shugaban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal, Farfesa Henry Ugboma ya sauka daga mukaminsa nan take saboda zargin almundahana da tsaurin ido.
Sa’annan a dawo da shugabannin reshen kungiyar na asibitin karkashin jagorancin Dakta Solomom Amadi, wadanda aka dakatar, ba tare da wani sharadi ba.
NARD ta ce taron nata ya yi nazarin yadda gwamnati ta mayar da hankali wajen biyan bukatun ‘ya’yanta tun bayan janye yakin aikin da suka shiga saboda matsalolin a baya.
Sai dai sun bayyana cewa gwamnati ta yi watsi da biyan wasu bukatun tun sadda ma’aikatan lafiyan suka janye yajin aikin.