Ƙungiyar Likitoci masu aiki da Gwamnatin Jihar Kano (NAGGMDP), ta yi barazanar tsunduma yajin aiki nan da makonni biyu masu zuwa idan har Gwamnatin Jihar ba ta biya musu wasu buƙatunsu ba.
Ƙungiyar ta bayanna cewa za ta shiga yajin aikin ne ranar 19 ga watan nan na Yuni a cikin takardar da ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Dokta Aminu Kabir.
- Hajjin Bana: Gwamnati ta ɗauki nauyin maniyyata 47 a Ribas
- An yi taron addu’o’i kan matsalar tsaro da tattalin arziki a Jigawa
A cewar takardar ƙungiyar ta ɗauki tsawon lokaci tana neman gwamnatin ta share musu hawaye amma ta yi biris da su.
Wasu daga cikin matsalolin da ‘ya’yan Ƙungiyar ke fuskanta sun haɗa da rashin samun yanayin aiki mai kyau, da rashin kayan aiki da kuma ƙarancin ma’aikatan lafiya.
Har ila yau, ƙungiyar ta koka kan rashin samun ƙarin albashinsu na shekara shekara (annual increment) na tsawon shekaru shida baya ga barazabar rashin tsaro da ‘ya’yan Ƙungiyar ke fuskanta a wasu asibitoci.
“Ko a kwanan nan wasu likitoci sun fuskanci irin wannan barazanar tsaro a yayin da suke bakin aiki a Asibitin Yara na Hasiya Bayero “
A cewarsa, har zuwa yanzu ’ya’yan ƙungiyar da gwamnatin ta ɗauka aiki su 61 ba su sami albashinsu na watan Oktoba da Nuwambar bara ba.
Ƙungiyar Likitocin ta ce har yanzu gwamnatin ba ta aiwatar da sabon tsarin biyan alawus din hatsarin aiki da na horarwa da wasu da dama wanda ta ce tuni Gwamnatin Tarayya da wasu jihohin suka fara aiwatar da shi.