Tawagar Kwararru Likitoci na Asibitin Sarki Abdullah da ke birnin Riyadh a Kasar Saudiyya, sun yi nasarar kammala aikin raba wasu tagwaye ’yan Najeriya, da aka haifa a manne da juna.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja, Mohammed Alsahabi, fitar a ranar Alhami.
Ya ce an yi nasarar raba tagwayen ne bayan tiyatar da aka yi ta tsawon sa’o’i 14, biyo bayan umarnin, Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da kuma masarautar Saudiyya.
An kai tagwayen Riyadh ne a ranar Talata 31 ga Oktoban 2023, inda aka musu gwaje-gwaje kafin sanya ranar yin aikin raba su.
Bincike ya nuna cewa jariran sun haɗu ne ta ƙashin ƙugu daga wani bangare na k8ashin baya da kuma wasu ƙananan jijiyoyi.
Alsahabi, ya bayyana cewa aikin tiyatar ya gudana ne a matakai tara da aka tsara tare da tawagar da ta kunshi kwararrun likitoci 38.
A cikinsu akwai masu ba da shawara, kwararrun masu fasaha, da kuma ma’aikatan jinya wadanda suka kware a fannin aikin jinya.
Wasu kuma na da kwarewwa a tiyatar yara, tiyatar kasusuwa, da kuma aikin jinyar yara don tabbatar da nasarar aikin nasu ba tare da matsala ba.
“Wannan aikin tiyata shi ne irinsa na 60 da ƙasar Saudiyya ta yi a wani shiri na musamman na raba tagwayen da aka haifa a haɗe.
“Shirin ya taimaka wajen yi wa tagwaye 135 daga kasashe 25 a cikin shekara 34 aiki.”
Mai ba da shawara a kotun masarautar, Dokta Abdullah Al Rabeea, ya bayyana kwarin gwiwarsa kafin yi wa tagwayen aiki.
“Dokta Al Rabeeah ya mika godiya da jinjina ga mahukuntan Kasar Saudiyya bisa goyon bayan da suka bai wa aikin.
“Wannan na nuna matsayin masarautar wajen ciyar da ilimin likitanci gaba da kuma aikin jin-kai a fannin kiwon lafiya a duniya baki daya.”