✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lawan ya bai wa waɗanda gobara ta shafa tallafin 10m a Yobe

Sanata Ahmad Lawan, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 10 don taimaka wa waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Bayan Tasha…

Sanata Ahmad Lawan, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 10 don taimaka wa waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Bayan Tasha da ke Jihar Yobe.

Gobarar, wadda ta faru a ranar Talatar da ta gabata, ta ƙone shaguna 46 tare da shafar sama da mutum 200 a Damaturu, Babban Birnin Jihar.

Tawagar da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Y’au Usman Dachia, ke jagoranta ta ziyarci wsjen don tantance asarar da ’yan kasuwar suka yi kafin bayar da tallafin.

Sanata Lawan, wanda ya samu wakilcin Alhaji Nasir Mato, Tsohon Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar United Market, ya nuna damuwarsa kan iftila’in.

Ya ce gobarar ta haifar da yanayi mara daɗi ga waɗanda abin ya shafa.

Ya buƙaci al’ummar Yobe su haɗa kai wajen taimaka wa waɗanda suka rasa dukiyoyinsu a gobarar.

Har ila yau, ya yi kira ga hukumomi da su gaggauta bai wa waɗanda lamarin ya shafa, agajin da ya dace.

Shugaban ’Yan Kasuwar Yobe Harmonies, Alhaji Muktar Kime, ya karɓi tallafin.

Ya gode wa Sanata Lawan bisa taimakon, inda ya bayyana cewa tallafin ya zo a kan gaɓa wajen taimaka wa ’yan kasuwar da suke ƙoƙarin farfaɗowa daga iftila’in da ya auku.