Logar layancewar lulaye
Limbu-limbun buzaye
Luggar bebaye
Lambun laujen lanjaye
Laulayin alayen lauye-lauye
Laulayin lauye-lauye
Laulawar lulaye
Lambatun masu alaye
Jimamamin jaye-jaye
Mahukunta sun yi maye
Fara’ar fuskokin furanni
Fatattakar fannoni
Farin dangon dausayi
Farmakin ga da tsautsayi
Fatanmu aiki da tunani
Sai an kawo sauyi
Ya ya za a yi
Mu hau bisa layi
Wasu ba su da tausayi
Garwashi ya zam gawayi
Sutura ta kamala
Ta haifar da takala
Tuntun kwarewa ta sagala
Lullubin ka ta makala
Kun ji sabuwar kutungwila
Na tsaya ina lalalala
Ko miyau zai malala
An hana lauya ta sakata ta wala
Ana ta yada juhala
An kauce wa adala
Matsiyata na bukatar bulala
’Yan wala-wala
Masu yada badala
Sai sun yi tsallen tsula
Tuni na cire musu hula
Ka ji kinbibi
Wai an hana daura kallabi
Ko sanya hijabi
Lamarin ba ya turbar adabi
dabi’un miyagu na da aibi
Kada a maishemu zabi
Masu bin labi-labi
Kan mai uwa da wabi
Kulorar ga akwai jangahur da zabibi
Dabarbarun ga ba sa cikin kitabi
Mun fasko masu haramta bobo
Da kwambo
Wai kada ai bokoko
Don kar mu sa mu na koko
Dabarar ga ba wani abu sabo
Mazan lauyoyi na da jallabiya
Matansu sanye da abaya
Tuntun ka tsororuwar kurya
Silin gashin makitsiya
A baza buya-buya
Kun ji aikin gaye-gaye
Kai duka ya kwaye
Buyagin baubawa ya zuganye
Masu ilimi kansu ya waye
Yau daliba tai muku tawaye
daliba ta samu kima
Da karin karama
Ai mata sallama
Ta samu salama
Kowa yai azama
An fasko masu karma-karma
Da ke ta tuma
Dundumin duman dama-dama
Masu jiji da kai da takama
Mugga masu halin kunama
Ana ta kai-kawo
Batutuwa babu awo
Dama-damar damun dawo
Juyin muciyar tukin tuwo
Wasan wutar kara wowo
Malam da malama
Mun gano masu takaddaama
Safe da yamma
Babu ko wata tantama
Mun ga kalma da kalama
Dukan dokoki
Bankar hayaki
Sai mai shan tabar buki
A runtumi auran shawaraki
Zabari ba burki
Kowa na da ’yanci
Ai tsaikon sasanci
A kiyayi rashin adalci
A daina duk wani batanci
Balle aikin ta’addanci
Ilimi ko ado
Tsarin rashin kangado
Rayuwar ramin kwado
Ko wasan kada ’ya’yan ludo
Tsunduma kogi ka tsunko bado
Mu bi doka
Kada kowa ya koka
Rani damina da kaka
A daina dan hankaka
A kiyayi warwarar tufka
karshen makon da ya arce na shiga birnin Dabo, inda ba a dabo, har ’yan dugwi-dugwi suka yi mini kabo da adabo, kodayake dai oyoyo Baba suka yi. Bayan da na kimtsa tsaf sai na fara bibiyar abin da aka tsuwurwurta a farfajiyar Balan-balan din sama, inda Fici da Bobo suka yi mini wake-wake, har ma da sauran nau’ukan watsattsake da buda wagagen littafai. Bayan mun kammala Bobo da kwambon bokoko sai na tuntubesu kan abin da suka koyo a Islamiyya nan da nan wata ’yar dugwi-dugwi da ke karatu kusa da gidan Maman Bebi can a tsaunin gwagware ta yi mini wani karatu, wai cewa:
A’ishatu fil Jami’a
A’isha ita ce mafificiya
Wannan likita ce
Waccan malama ce
Kai bari in kara:
Waccan lauya ce
Ana ta yi mata ce-ce-ku-ce
Ilimi da hijabi an yi kawance
Ni dai iyakata kwatance
Haurobiyawa sun iya zaurance
Hakika batun ’yar karama mai bobo da kwambon bokoko da sallama da salama a Islamiyya ya yi matukar burgeni, don haka ma na jadadda cewa lallai a biya direbobin alli da malaman Islamiyya ladar la’adar kwadago ko da da kadago ne, ba tare da la’akari da wulwulawar agogo ba.
’Yan makarantar Dodorido ba so nike in cika ku da surutu rututu ba, musamman jin cewa A’isha ita ce a jami’ar, kamar yadda karamar ’yar dugwi-dugwi ta rera mini, illa dai kawai ina son nusar da ku wani muhimmin lamari da ya dugunzuma ni cikin dundumin damuiwa, wato LAULAYIN LAULAWAR ALAYEN LAUYE-LAUYEN DOKOKI a kasar Haurobiya, musamman yadda na ji kafafen yada kwakwazo ana ta yamadidi da wata daliba Amosa Firdausi ’yar AbdusSalam da ta zo karbar shaidar kwarewarta aka hanata, wai saboda ta yi lullubin kai, sannnan ta dora tuntun kwarewar lauye-lauyen dokoki a sama.
Lamarin lauya mai kallabi ya kara tabbatar mini akwai miyagun boye da ke kokarin HARAMTA BOBO DA kWAMBON BOKOKO. Ni dai na fada na kara fada AI BOBO DA kWAMBO SAI dAN BOKO. Ina nan a garin TAKO-TAKO CIKIN dAKIN KATAKO ina lalube NA-KOKO in ga wanda zai zo ya haramta mini Bokokon!
Hakika an yi wa wannan lauya ta’addanci a daidai lokacin da ake ta fafutikar tabbatar da ’yanci babu ’yan cici. Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo kada ku bari a yi ta rawar banjo kan wannan lamarin, domin Baba-Ojo ya kammala digirin-digirgir a jam’in jama’ar jami’ar karatun dogon zango.
Haurobiyawa lokaci ya yi da za mu fifita sanya sutura ta kamala bisa tsarin al’adunmu, ba tare da mun cusguna wa wani ba. Idan kuwa an yi wa dokoki ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege, wajibi ne a nusar da mu, ta yadda za mu tsige ’ya’yanmu daga makarantun da ke tauye hakkokin al’umma a duk sa’adda suka kammala jami’a.
Ni dai nasan a daukacin fadin duniya Jam’in jama’ar jami’o’i ke yaye zakakuran direbobin alli, wadanda a kodayaushe suke horar da masu lauye-lauyen dokoki don tabbatar da ’yanci, ta yarda za a kauce wa shiga kunci. Haurobiyawa kada mu yi butulci, wannan aikin wawanci ne a karni na karamin lauje da sili. Ko so ake yi mu rika bobo da kwambo da walki ko mu tube zigidir, har da an hango mu a ce ahir ko ma wasu su ce tur?! To haihata-haihata atafau ba zan yarda da tafka ta’asa irin wannan ba, musamman a farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da mujallu da makalu da jaridu da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar nan.