Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya roki Gwamnatinn Tarayya da ta daga likafar cibiyar dankalin Turawa da ke Bukuru a jihar zuwa cikakkiyar cibiyar bincike.
Lalong ya yi rokon ne ranar Alhamis yayin jawabinsa a bikin bude taron Majalisar Noma da Raya Karkara ta Kasa da yake gudana a Jos, babban birnin jihar.
Gwamnan ya ce bukatar kafa cibiyar ta zama wajibi la’akari da yadda ake kara samun sabbin cututtukan da suke kama dankalin.
Ya ce kwatankwacin irin wannan cutar da dankalin ya yi a bana ta sa manomansa sun tafka mummunar asara.
Ya kuma ce, “Kafa sabuwar cibiyar zai taimaka matuka wajen fito da sabbin dabaru a bagaren bincike, samar da iri da kuma magance cututtukan da ke shafar dankalin.
“Za kuma ta taimaka wajen bunkasa ilimin manoma, sannan ta kasance wani tsani tsakanin cibiyoyin bincike na cikin gida da takwarorinsu na ketare.
“Yanzu haka, mun gudanar da bincike, inda muka gano cewa za a iya noma dankalin da aka samarwa yanzu haka a yankin Tsakiya da kuma Arewacin Filato a kananan hukumomin 17 na jihar.
“Jihar Filato ce take noma kaso 90 cikin 100 na dankalin Turawan da ake ci a kasar nan, saboda haka nake ganin kafa wannnan cibiyar binciken na da muhimmanci sosai,” inji Gwamnan.
Gwamnan ya kuma ce a tsawon shekara bakwai din da ya shafe a matsayin Gwamnan jihar, gwamnatinsa ta ba aikin gona muhimmanci kwarai da gaske.