Kotun Shari’a ta Lardi da ke Dutse a karkashin jagorancin Mai shari’a Yahaya Ibrahim Yayari ta yanke wa matashin nan mai suna Ahmed Muhammed da aka kama da laifin yi wa wata matar aure ciki hukuncin bulala 100 da tarar Naira dubu 30 da kuma biya matar da ya yi cikin Naira dubu 50 kudin ciyarwa bayan samunsa da laifin yin zina.
Da yake yanke hukuncin Mai shari’a Yahaya Yayari ya ce kotu ta yi la’akari da cewa wanda ya aikata laifin zinar ba ya da aure, kuma bai taba aikata laifi makamancin haka ba kuma yana daf da zana jarrabawarsa ta fita daga sakandire saboda haka ne ta yi masa sassuci a hukunci amma laifin da ya yi bayan bulala 100 ya ci a aika da shi gidan maza ba tare da zabin biyan tara ba.
Alkalin ya ce matar waddda shekarunta ba su wuce 14 ba, saboda ta janye ikirarinta na farko kuma tana da ciki za ta biya tarar Naira dubu 20 kuma za a yi mata bulala bayan likita ya bayar da bayanin za ta ita daukar bulalar in kuma aka samu akasin haka bayan ta haife za a yi mata bulala 30 a bainar jama’a.
Tunda farko Lauyan Ahmed, Barista Bashir Hussain ya roki kotun ta yi wa wanda ake tuhumar sassauci saboda dalibi ne a makarantar sakandare kuma yana dab da fara jarrabawar kammala makaranta kuma wannan ne laifinsa na farko kuma yana da karancin shekaru, inda ya bukaci kotun da mayar da hukuncin dauri zuwa tara.
Kotun ta ba su damar daukaka kara idan ba su gamsu da hukuncin da aka yi musu ba daga nan zuwa wata daya.