✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lakwaja: Birnin da manyan kogunan Nijeriya suka haɗu amma ba ruwan sha

Ana ɗauko motocin dakon ruwa domin yankunan da ke fama da mugun ƙarancin ruwan sha.

Babu shakka, ruwa, abokin aiki cikin kowane yanayi ɗan Adam ya kasance a rayuwa yana buƙatar ruwan sha. Rashinsa na sa rayuwa ta zama mara amfani a cikin yanayin halitta.

Amma wani abin mamaki, shi ne mazauna Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi birnin da ke da manyan koguna biyu; Kogi Kwara (Kogin Neja) da Kogin Binuwai, amma duk da haka mazauna birnin sun daɗe suna fama da ƙarancin ruwan sha.

A cewar Dokta Yahaya Abdullai, wani darakta mai ritaya a ma’aikatar gwamnati a jihar, abin takaici ne ga mazauna Lakwaja masu irin wannan baiwa a ce suna ci gaba da fama da ƙarancin ruwan sha.

Ya ce abin takaici ne ganin yadda jama’a ke taruwa a ɗaruruwa don neman ruwan sha a rijiyoyin burtsatse ko wasu wuraren da ke Lakwaja.

“Abin takaicin ma babu kamar yadda mazauna garin Lakwaja ke yawo kwararo-kwararo, lungu da saƙo da sunan neman ruwan sha, wasu ɗauke da kwatarniya wasu jarkoki ko bokitai da sauransu.

“Ko ka ga motoci ɗauke da garewani da tuluna iri-iri, suna yawon neman ruwan sha a wurare daban-daban a babban birnin,” in ji shi.

Dokta Abdullahi ya ƙara da cewa, “Da yawan mutanen birnin sun rungumi ƙaddara; kamar yadda tsarin ruwa na jama’a ya kusan rushewa kuma famfunan ruwa suka bushe da yawa suka ƙafe a wurare daban-daban tsawon shekaru.

Masu aikin rijiyoyin burtsatse da masu sayar da ruwa ne suka mamaye wurare da yawa a birnin suna cin karesu ba babbaka, inda suke ƙara farashin kowace lita na ruwa ba tare da la’akari da halin da jama’a ke ciki ba.”

A cikin wahalhalun da ba za a iya tantancewa ba, da matsalar ƙarancin ruwan ta haifar a Lakwaja babban birnin Jihar Kogi, ana samu haɗarurruka da kamuwa da cututtuka sakamakon rashin ruwan.

An bayar da rahoton cewa mutane da dama sun rasa ’yan uwansu sakamakon haɗɗurran da suka haɗu da su a lokacin da suke neman ruwan, wasu da dama kuma sai dai su yashe asusun ajiyarsu na banki ko su fita waje suna roƙon a taimaka musu don su biya kuɗaɗen jinya a asibiti sakamakon cututtukan da ’yan uwansu suka kamu da su saboda rashin tsabtataccen ruwa a irin wannan yanayi.

“Kwanan nan, wani mutum a unguwar Aniebo daura da garin Gadumo-Lokoja ya kusan rasa ’yarsa Jummai mai shekara 17, wadda ta je neman ruwan sha a wata unguwa.

“Wani mutum a kan babur, cikin tsananin gudu ya buge ta, a lokacin da take tsallaka babbar hanya. Ta ɗauki tsawon wata tana jinya kafin ta warke daga raunukan da ta samu.

“Irin waɗannan munanan labarai, sun yawaita a cikin birnin, in ji Onuh Godwin, mazaunin rukunin gidajen da ake kira Aniebo Kwatas.”

Haka, wata manaja mai kula da gidan abinci, Hajiya Salamatu Abubakar wadda take zaune a Adankolo-Lokoja ta ce: “A bara, wata mata mai ’ya’ya bakwai da take zaune a gaɓar Kogin Neja a Adankolo­Lokoja ita da ’ya’yan sun yi kusan mutuwa sakamakon kamuwa da cutar kwalara saboda ci gaba da shan gurɓataccen ruwan Kogin Neja mai cike da ƙazanta.”

Matsalar ƙarancin ruwan sha sanannen abu ne a yankunan birnin irin su Kabawa, Madabo, Lokoja New Layout, Gadumo da Lokogoma, Phase1 da 11, Peace Community da Ganaja-Lokoja da garin Ganaja­Lokoja da kuma yankunan Mounti Patti a Lakwaja da sauransu.

Mazauna garin Lakwaja masu dukiya da masu kishin addini suna tona rijiyoyin burtsatse don biyan buƙatun kansu da iyalansu, yayin da wasu ke gina rijiyoyin burtsatsen don kasuwanci, suna kuma sa tsada a kan kowace litar ruwa.

“Wannan mummunan lamari ne da ya daɗe a Lakwaja yadda ake kallo ba a yin komai a kai, shi ne yadda a da ake sayar da jarkar ruwa mai cin lita huɗu a tsakanin Naira 20 zuwa 50 a baya dangane da tazarar da ake samu, amma a yanzu ta koma Naira N200 a mafi yawan sassan birnin.

“A wasu lokuta, saboda yawan buƙatar ruwan daga masu sayar da ruwa, abokan ciniki kan yi rajista na kwanaki kafin a kai musu ruwan. A mafi yawan lokuta, irin waɗannan alƙawura da ake yi da masu ruwan ba sa cikawa.

Saboda haka ya zama dole ne mu rufe shaguna na kwanaki har sai mun samu ruwan,” in ji Maman Chioma, wata ma’aikaciyar wani shahararren kantin sayar da abinci a Lakwaja.

Wani mai sayar da ruwa, Malam Zubair Rufa’i ya danganta ƙarin kuɗin ruwa da ƙarin kuɗin man fetur, inda ya ce hakan ya yi tasiri a kan yadda suke bi su ɗebo ruwan da kuma nisan inda za su kai.

“Madogarar da hukuma ke samar da ruwan sha ga jama’a a Lakwaja ta ruguje.

“Yanzu muna samun ruwanmu daga masu aikin rijiyoyin burtsatse masu zaman kansu ne, waɗanda suka ƙara farashin kowace lita.

“Ba mu da wani zaɓi illa mu ƙara namu don biyan kuɗin ruwa a majiyar,” in ji Rufa’i.

A wani lokaci, gwamnati musamman a farkon wannan shekara, sai da ta sa aka yi gyara aka ɗauko motocin dakon ruwa don rarraba ruwa ga yankunan da ke fama da mugun ƙarancin ruwan sha.

Mazauna yankuna da dama sun yaba ƙoƙarin da gwamnatin ta yi a wannan fanni amma sun bayyana shi a matsayin ɗigon ruwa ne kawai a cikin teku, suna masu cewa, mazauna yankin kaɗan ne suke amfana da wannan shiri na rarraba ruwa ga jama’a.

“Gwamnati ta ɓullo da tsarin samar da ruwan ta tankoki a matsayin yunƙuri na daƙile matsalar ƙarancin ruwan sha a wasu yankuna na Lakwaja.

“Lamarin da ya zama waɗanda suke zaune a bakin tituna kaɗan ne suke amfana, kuma mazauna tituna da yawa suna dai jin labarin ƙoƙarin da ake yi, amma ba su ga ruwan ba tunda bai isa gare su ba,” in ji mutanen da dama.

Suka ce “Muna ganin haka a matsayin fargar jaji da ba ta da wani tasiri kan halin da ake ciki.”

Injiniya Ahmadu Babajide ya ce “Maganin ƙarancin ruwan sha a Lakwaja mai ɗorewa shi ne a fara aiki a Babbar Tashar samar da ruwan sha ta Lakwaja, wadda tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Idris ya haɗa, wadda aka ce ta ruguje a lokacin gyara ta.

“Kuma a sake farfaɗo da matatun ruwa guda biyu,” in ji Injiniya Ahmadu Babajide, wanda ya yi iƙirarin cewa yana cikin ayarin injiniyoyin da suka haɗa babbar tashar ruwa ta Lakwaja.

A ƙoƙarinsa na samar da ruwan sha a Lakwaja, tsohon Gwamna Ibrahim Idris da haɗin gwiwar wani mai sa hannun jari na ƙasar China suka gina ‘The Greater Water Works’ a Lakwaja.

Kamfanin Ruwa na Lakwaja da ke gaɓar Kogin Neja a yankin Ganaja­Lokoja, an sa masa kayan aikin da ake buƙata don gudanar da aikinsa yadda ya kamata a kowane ɓangare na birnin, gami da isassun kuɗaɗe don sauƙaƙa ayyukansa.

Injiniya Ahmadu Babajide, wanda ya yi iƙirarin cewa ya taka rawar gani a aikin, ya ce da aka haɗa a wancan lokacin ba da jimawa ba ya fara aiki a aka samu ruwa.

Kash, sai dai da ya fuskanci matsalar ambaliyar ruwa wadda ta kawo cikas ga gudanar da ayyukansa yadda ya kamata saboda ɓarnar da ambaliyar ta yi.

“A cikin ƙalubalen da aka samu saboda ɓarnar ambaliyar wadda ta nutsar da wasu muhimman kayan aikin masana’antar tare da “raguza” su, tsarin da aka yi na wata-wata don ci gaba da ba da ruwa ya ragu sosai saboda tsarin gwamnatin da ta gaji tasa, tare da tsoma bakin wasu masu faɗa-a-ji da wasu ƙungiyoyi masu neman biyan buƙatunsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, sauran cibiyoyin kula da ruwa guda biyu da ke hanyar Marine Road da Felele-Lakwaja sun tsufa, wanda hakan ya sa ba sa iya bayar da ruwa yadda ta kamata.

A baya an sanya tsofaffin na’urorin da suka rage aka yi amfani da su zuwa wani lokaci kaɗan su ma suka gaji suka tsaya.

Mazauna yankin da dama sun ce ko a lokacin da ake ƙololuwar aikin, ‘Babban Gidan Ruwa na Lakwaja’ ba ya iya raba ruwa isashshe ga mutane kowa ya amfana, saboda an lalata manyan layukan ruwa da bututun ruwa a lokacin aikin gyaran manyan titunan Lakwaja.

A cewar mazauna yankin Lokogoma-Lokoja, mafi yawan bututun da ke haɗa manyan layukan da ke bayar da ruwa, manyan injuna ne suka katse su a lokacin da ake aikin samar da magudanun ruwa da kuma gyaran babbar hanyar Ganaja zuwa barikin sojoji daga mahaɗar shiyya ta 8 a gefen birnin.

“Tun kafin tsarin aikin ruwa ya ruguje, ba mu samun ruwa a Lokogoma Kashi na Ɗaya da Kashi na Biyu a Lakwaja.

“Akasarin bututun ruwan da suka maƙale a babban layin da ke yankinmu sun lalace kuma babu wanda zai maye gurbinsu duk da ci gaba da kai rahoto ga hukumar da abin ya shafa,” in ji Misis Rabiyatu Jibrin, wata mazauniyar yankin.

Sai dai ga dukkan alamu babu ranar kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwa a Lakwaja.

Kuma gwamnatin Jihar Kogi ta danganta lamarin da matsalar ɗumamar yanayi da ke haifar da ambaliyar ruwa, wanda ya yi sanadiyyar lalata kayayyakin samar da ruwan shan da na more rayuwa

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kogi, Injiniya Yahaya Farouk, ya ce sakamakon sauyin yanayi ya sa babbar tashar samar da ruwa ta Lakwaja ta samu cikas ga samar da ruwan sha ga mazauna birnin Lakwaja.

Ya ce, ambaliyar ruwa mai yawa a shekarar 2022, ta lalata manyan sassan babban kamfanin samar da ruwa na jihar, wanda aka gina a shekarar 2010, mai ƙarfin samar da ruwan sha galan miliyan 15 ga jama’a a kowace rana.

Injiniya Farouk ya ƙara da cewa ambaliyar shekarar 2022 ta lalata famfunan tuƙa-tuƙa guda shida daga cikin takwas, tare da lalata babbar tashar ruwan, ɗakin sinadarai da sauran muhimman abubuwan da ake haɗa ruwa da su.

“Rushewar matatar ruwa da ‘mummunar ambaliyar ruwa’ ta haifar da ƙarancin ruwan da ake fama da shi a babban birnin jihar a halin yanzu.

“Mafi girman aikin ruwa na Lakwaja, shi ne wanda ke da ƙarfin samar da galan miliyan 15 na ruwan sha a kowace rana, yana samar da galan miliyan 10 na ruwa zuwa birnin Lakwaja, kafin ya lalace,” in ji shi.

Kwamishinan wanda ya ce aikin ruwan na buƙatar matakai uku na farfaɗo da muhallin saboda ɗimbin ɓarnar da ginin ya yi, ya nanata cewa gwamnatin jihar ta yanke shawarar tuntuɓar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabtar Muhalli ta Tarayya domin ta ta shiga tsakani ta taimaka musu, ƙari kan wasu matakai masu yawa da gwamnatin ta ɗauka na shawo kan lamarin.

Ya ce mayar da ayyukan ruwa zuwa wani wuri mai tudu, inda ambaliya ba za ta lalata ba shi ne suke gani mafi kyawun zaɓi da zai magance matsalar, amma wannan aiki zai ci kuɗi tsakanin Naira biliyan 120 zuwa Naira biliyan 150.

A halin da ake ciki kuma, a matsayin ma’auni na wucin-gadi, ya ce ana sake farfaɗo da tsohon Kamfanin Ruwa na Lakwaja, mai ƙarfin samar da kubic mita 200 a kowace rana don zama madogara ga ‘gyaran aikin samar da ruwan sha na Lakwaja da ake yi.

Ya tabbatar wa mazauna Lakwaja cewa, tsohon gidan ruwa na Lakwaja ya shirya tsaf don samar da ruwa kimanin galan miliyan ɗaya ga mazauna Lakwaja a watan Yuli, domin gwamnati mai ci ta himmatu wajen kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwan.