Akalla mutane 300 ne suka mutu a Birnin Freetown, babban birnin Saliyo, bayan da laka ta binne wasu gidajen da ke wani yankin birnin.
BBC ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a yankin Regent da sanyin safiyar Litinin bayan ruwan sama mai kama da bakin kwarya, kuma lakar ta binne gidaje da yawa.
Wakilin BBC da ya ziyarci wurin ya ce da alama mutane da dama na barci a lokacin da zabtarewar lakar ya faru.
Kawo yanzu ba a san yawan wadanda lamarin ya rutsa da su ba, amma mataimakin shugaban kasar Saliyo, bictor Bockarie Foh, ya ce “akwai yiwuwar daruruwan mutane sun halaka”.
Mista Foh ya fada wa Reuters cewa bala’in “ya gigita ni gaba daya”, inda ya kara da cewa an killace yankin domin gudanar da ayyukan ceto.
Kamfanin dillacin labarai na AFP na bada rahoton cewa akalla mutum 180 suka mutu. Kawo yanzu an gano gawawwaki da dama.
kungiyoyin masu ba da agaji sun je wurin domin ceto wadanda lakar ta birne a cikin gidajensu, bayan da wani bangare na dutsen ya zabtare, inji wani rahoton jaridar Sierra Leone Telegraph.
Hotunan da aka wallafa a Twitter sun nuna mutane na tafiya cikin titunan yankin cikin tabon da ya kai kugunsu bayan ruwan saman da ak yi a kusa da birnin Freetown.
A kan sami irin wannan ambaliyar ruwa a yankin birnin na Freetown, inda rashin ingantattun gine-gine kan sa ruwan ya tafi da muhallai da dama bayan ruwan sama mai yawa.
A shekarar 2015, birnin Freetown ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa bayan wata guguwar da ta hada da ruwan sama ya janyo mutuwar mutane 10 kuma dubbai suka rasa muhallansu.