✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Warware Husumar Aure (11)

Assalamu AlaIkum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu AlaIkum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magance su.  Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Hanyoyin Magance Karkataccen Kishin Uwar Miji, (Cigaba)…
Abinda Uwargida za ta iya yi: In uwargida ta fahimci bayyanar karkataccen kishi daga wajen surukarta:
· Abu na farko da za ta fara yi don magance wannan al’amari, shi ne yin matukar hakuri da dukkan wasu dabi’u da za su bayyana daga wajen suruka.  Kai zuciya nesa game da al’amarin ta hanyar sawa a ranta cewa sannu a hankali wata rana hakan zai zama kamar ba a  yi ba.   Da kawar da kai daga dukkan abubuwan bacin rai da za su bayyana da kuma danne zuciyarta don ganin cewa wadannan abubuwan ba su kai ta ga bayyanar da wasu dabi’ u marasa kyau ba, kamar rashin kunya da rashin kyautatawa da sauransu.
· Sannan uwargida ta fahimci cewa mahaifiyar maigidanta ta fi kowa muhimmanci a rayuwarsa. Farin ciki ko bakin ciki da suka same ta a dalilinsa na da nasaba a rayuwarsa a zahirance da badinance; sannan a duniyance da a lahirance; don haka in har kaunar da take wa maigidanta ta gaskiya ce, to dole ta zama mai kokarin samar da zaman lafiya tsakaninta da mahaifiyarsa; kamar yadda ta san ba ta son ta samu sabani tsakaninta da nata iyayen to shi ma maigida sai ta zamar masa jakadiyar samar da zaman lafiya da neman albarka tsakaninsa da iyayensa; ba ya kasancea a dalilin zama da itane yake yawan samun sabani da iyayensa ba.
· Uwargida ta yi kyakyawan nazari ga dabi’unta, na maigidanta, na iyali duka da yanayin zamantakewa gaba daya. Ta fahimci wadanda suke zama barazana ga surukarta har suke sa ta bayyanar da karkataccen kishinta, sai a bi hanya mafi dacewa don magancesu, ko dai a canzasu, ko a boye su daga ganin idonta ko a dakatar da su gaba daya.
· Uwargida ki fahimci cewa Surukarki ba dai-dai take da mahaifiyarki ba, in kika ce za ki huldance ta a yadda za ki huldanci mahaifiyarki dole a samu matsaloli sosai, domin mahaifiyarki ta fi kowa saninki da fahimtarki; sannan ta fi kowa kawar da kai ga kura-kurenki da raunukanki; don haka in kika ce za ki dauki surakarki irin daukar da kike wa mahaifiyarki; kamar kina nufin ita ma ta rika kawar da kanta daga kurakurenki da raunukanki; wanda abune mai wuyar gaske domin ba ta sanki ba, kuma ba ta fahimceki ba irin yadda mahaifiyarki ta fahimceki kuma ta sanki. Kuma kar ki sa a ranki lallai sai ta rika yi maki yadda take ma ’ya’yanta mata da ta haifa a cikinta; domin ta sansu ta fahimcesu, don haka ta riga ta saba da sadaukarwa da kawar da kai ga kura-kurensu sama dake, da kika zo mata da rana tsaka.
· Ba a samun kyakykyawar fahimtar juna tsakanin mutum biyu dole sai ya kasance akwai kyakykyawar kafar sadarwa a tsakaninsu; don haka a lokacin da kike cikin more rayuwar aure da dan surukarki; sai kiyi kokarin shuka kyakykyawar danganta tsakaninki da surukarki ta hanyar bata lokacinki wajen yin hira da ita, yi mata ayyukan kyautatawa, neman taimakonta da neman shawararta.  
Abinda suruka za ta iya yi:
In Uwa ta fahimci bayyanar karkataccen kishi a cikin zuciyarta game da matar danta; tun kafin abin ya yi nisa ya kai ga bayyana cikin ayyukanta da dabi’unta sai ta mike tsaye ta yaki wannan bakin shauki ta wadannan hanyoyin:
· Ta fara da neman taimakon Allah SWT don ganin ta samu ikon yakar shedan don kawar da wutar bakin shauki daga zuciyarta; ta hanyar kyautata niyya, yawan zikiri da kyautata ibadunta.
· Abu na biyu da Uwa za ta yi shi ne ta yi kokarin tsare mutuncin kanta da na danta; domin ba kyautuwar mutuncinta ba ne a ce tana kishi ko ganin kyashin matar danta. Haka nan shi dan nata ba kyautuwar mutuncin shi ba ne a ce mahaifiyarsa tana gasa da matarshi game da shi. Don haka ko don gudun bakin duniya sai uwa ta yi hakuri ta kawar da kanta daga al’amuran da ba su shafe ta ba game zamantakewar danta da matarsa.
· Uwa ta fahimci cewa tun daga ranar da danta ya yi aure, to nauyin kula da shi ya sauka gaba daya daga kafadarta ya koma kan matarsa, don haka sai ta yi hakuri ta ja girmanta ta bar matar nan ta yi zaman aurenta lafiya da mijinta; in har da gaske tana kaunar danta, to dole ta daure ta daina takura wa matarsa, ta fita harkarta gaba daya ya kasance tsakaninsu sai gaisuwar arziki da hirar mutunci kada. Ta yi hakuri ta daina kokarin sa mata ido kullum tana neman laifinta ko inda ta yi kuskure.
Sai sati na gaba in sha Allah.   Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa akodayaushe, amin.