✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Warware Husuma Auratayya (6)

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan husumar auratayya da hanyoyin da za a bi don magancesu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
9. Matsalolin Surukkuta: Matsalolin da suka samo asali daga surukan miji ko na mata na yin babban rauni ga zamantakewar ma’aurata wata sa’in har hakan ya kai ga mutuwar aure, wannan yana faruwa ne saboda girman ikon iyaye da kuma darajar da suke da ita a idon ’ya’yansu; ga bayani kan manyan sinadaran da suke yawan haifar da matsaloli cikin surukkutar aure:
1. Wuce gona da iri ta bangaren surukkai: Yanayin canzawar zamani ya sanya surukai yanzu suna kutsa kai da wuce iyaka cikin al’amuran auren ’ya’yansu ta hanyar dake haifar da matsaloli ga ma’auratan. Wannan ya danganci tsoma baki ko cusa kai cikin abubuwan da ba su shafe su ba a cikin rayuwar auren ’ya’yasu; da wuce wuri wajen nuna iko da bayar da umarni kan abubuwan da suka wuce ka’ida; da kuma kokarin nuna karfin mulkin mallaka akan ’ya’yansu sama da abinda yake shine ka’ida ko shine mafi dacewa. Wasu iyaye suna sa ka’idoji akan ’ya’yansu game da iyalansu wadanda basu da wani alfanu da ya wuce na nuna isarsu da mallakarsu akan ’ya’yan nasu.
Maganin: Makarin wannan dafin a cikin rayuwar aure shine iyaye su san iyakarsu a cikin rayuwar auren ’ya’yansu; su rike girmansu kuma su ja mutuncinsu, su bar tsoma baki a cikin yanayin zamantakewar auren ’ya’yansu sai a inda ya zama dolen-dole su tsoma bakin ko a inda aka nemi jin ta bakinsu. Su sani cewa ’ya’yansu yanzu ba kananan yara bane, sun mallaki hankalin kansu da zasu iya gudanar da rayuwarsu ba tare da sa idon mahaifansu ba; don haka su sakkar masu mara su barsu su wala da ma’auransu ba tare da sa ido da tsangwama ba. Babban abinda yara suke bukata a wannan lokacin shine kyakykyawar addu’a da nasiha daga wajen iyayensu; in iyaye suka lura ko suka ji labarin wani abu da bai dace ba a cikin yanayin zamantakewar auren ’ya’yansu, abinda yafi dacewa shine sai su nemi jin ba’asinsu, in har ya tabbata haka din ne, to sai suyi masu nasiha su kuma gargade game da abin, amma ba su su shiga ko ina suyi kaka gida cikin auren ’ya’yansu ba; aure tsakanin mutum biyu kadai ake daura shi, duk lokacin da wani na ukku ya kutsa kai a ciki sai an sami matsala. Sannan iyaye su runka cire rai akan abin hannun ’ya’yansu matukar suna da halin kula da kansu, sannan kuma su daure su daina jin kyashin hidimar da yake yi ma iyalansa, kuma su daina kishin lokaci da kulawarsa ga iyalansa, wannan shine sinadarin zaman lafiya da kwanciyar hankalinsu gabadaya. Sannan su runka kai ziyara ta sada zumunci ga ’ya’yansu da surukkansu suna bincikar yanayin zamantakewarsu, in sun ji akwai matsala sai suyi kokarin warwareta, in kuma sun tarar da wata ’yar hatsaniya sai suyi kokarin yi masu sulhu; yin haka Sunnah ce Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi; kamar yadda yazo a ingantattun Hadissai cewa Yana tsiyartar ’Yarsa Fatimah Allah Ya kara yarda a gareta a gidan aurenta don sada zumunci kuma don jin halin zamantakewarta da Mijinta, Allah Ya kara masa yarda. Haka kuma wasu daga cikin Sahabbai, Allah Ya kara masu yarda sun aikata irin haka a lokacin rayuwarsu. Don haka wannan shine abin koyi kuma abin aikata ba biye ma son zuciya da zugar shaydan ba.
Shi kuma Maigida ya sani cewa hakkin iyayensa yana sama da na iyalensa, don haka yayi dukkan kokari ya ga ya sauke masu dukkanin hakkinsu dai-dai iyawarsa, ta yadda basu da wani dalilin da zai su runka yawan korafi game da shi ko game da zamantkewarsa da iyalensa. Sannan yana daga cikin hakkinsu a gareshi in sun yi kuskure yayi kokarin hankaltar dasu ta kyakykyawar  siga ta yarda zasu fahimci kuskurensu su kuma gyara; ba dai-dai bane magidanci ya kyale mahaifansa suna yin abubuwan cutaswa ga iyalansu amma yasa masu ido da nufin yi masu biyayya da girmamawa; wannan biyayya ce da zata cutar dasu ba zata amfanesu ba, domin shiga hakkin matar dansu da suka yi, yana nan a matsayinsa na shiga hakki kuma laifi ne a wajen Allah Madaukakin Sarki dan haka dole, ko ba don matar ba, don raba mahaifansa da nauyin wannan hakkin, magidanci ya ganar da iyayensa kuskurensu yayin da suka zartas da wani abu da ya zama cutaswa ga iyalinsa.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Yasa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.