✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Warware Husuma Auratayya (3)

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban makalar kan Husumar Auratayya da Hanyoyin da za abi don maganceta; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su.
4.    dawainiyar Auratayya: Sauye-sauye da aure kan dora a kan rayuwar ma’aurata yana daga cikin manyan abubuwan da suke haifar da husuma cikin zamantakewar aure; musamman ta fannin shigowar sabbin dawainiya a kan ma’aurata wadanda da can babu su. Nauyin fadi-tashin ciyarwa, tufatarwa, tarbiyya da tsare mutuncin uwargida da suka fada kan maigida; da nauyin kula da gida, ladabi da biyayya ga maigida; nauyin ibadar aure da nauyin daukar ciki, haihuwa da kula da yara da suke fadowa kan uwargida bayan aure duk suna haduwa su haifar da wani matsatsi da takurawa ga ma’aurata wadanda ke gajiyar da ma’aikatar hankali; don haka abin da bai kai ya kawo ba, sai ya zama sanadiyyar kace-nace da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin ma’aurata.
Magani: Kamar yadda Hausawa kan ce hakuri maganin zaman duniya; to haka kuma hakuri shi ne maganin zamantakewar aure. Ma’aurata su yi hakuri da nauyin aure da kuma sauye-sauyen da aure ya dora a kansu. Kar wani nauyi ko wani sauyi da ya fado kan ma’aurata cikin rayuwar aurensu ya sa su kasa hakuri su rinka tayar da jijiyoyin wuya a dalilin haka. duk wani matsatsi da nauyi da igiyar auratayya ta haifar a dauke shi a matsayin abu ne mai wucewa don haka sai ayi hakuri da shi har ya wuce. Sannan ma’aurata su ba lafiyar zamantakewar aurensu matsayi sama da dan wani sabawa na tsakanin harshe da hakori, sama da daidai da ra’ayin junansu. Idan wani bacin rai ya gitta, ko wani sabani ya faru, kowanne ya aje ra’ayinsa a gefe daya a dauki ra’ayin da zai haifar da zaman lafiyar zamantakewar aure.
5.    Matsalolin iyali: Matsalolin da nauyi da karuwar iyali ke haifarwa na zama dalilin sarkewar gardamar da ka iya zama dalilin faruwar husuma a tsakanin ma’aurata. Misalin haka kamar idan aka sami bambanci a kan yanayin zamantakewar iyali, miji yana son a runka yin abu kaza, ita kuma mata ta ji yin haka takurawa ne a gareta ko ta ji ita wani abin take so ayi daban; ko ma’aurata su sami bambanci mai girman gaske a kan kula da gida, kula da yara, tarbiyyar yara da sauransu; duk wadannan sinadarai ne da ke iya zama ashanar kunna wutar husuma tsakanin ma’aurata.
Magani:
Maganin da zai kashe dafin wannan sinadari a cikin zamantakewar aure shi ne ma’aurata su tanadi kyakykyawan shiri da kyakykyawan tsarin don ci gaban iyalinsu. Su zauna su tattauna su tsara abubuwan iyalinsu dai-dai da yanayinsu da kuma bukatunsu, kuma kamar yadda na fada a sama, su aje tsarin da ya yi daidai da ra’ayinsu, su dauki tsarin da ya yi dai-dai da inganta zamantakewar iyalinsu. Sannan su yi hakuri, suyi juriya da dauriya wajen zartar da abin da zai kawo ci gaba a cikin rayuwar iyalinsu. Sannan su runka kokarin kau da kai ga kananan kura-kuren juna; kuma su runka hakuri da halin yau da kullum da irin tasirin da hakan zai yi cikin rayuwar iyalinsu. Sannan su dage da addu’a, ba dare, ba rana ga Allah Ya azurta su da tabbataccen aminci cikin rayuwar iyalinsu.
6.    Matsalolin ibadar aure: Wannan yana jagaba cikin sinadaran da suke haifar da husuma a cikin rayuwar aure; kuma shi ne jagaba a cikin abubuwa da suke zama sanadiyyar mutuwar aure tsakanin ma’aurata. Wadannan matsaloli sukan bullo ta banagaren maigida da kuma ta bangaren uwargida. Amma wadanda suka bullo ta bagaren maigida ba su cika haifar da husuma ba ko mutuwar aure; domin da yawan mata suna hakuri da matsalolin mazajensu ta wannan bangaren, amman maza kadan ne ke hakuri da matsalar ibadar aure daga wurin matayensu.
Magani: Maganin wannan matsala shi ne ma’aurata su dauki kan su a matsayin daya, don haka duk matsalar da ta sami daya kamar ta sami dayan ne, sai su hada kai su taru wajen neman maganin warke matsalar, kar su bari hakan yasa su runka jin haushin abokin aurensu, su runka ganin ai laifinsa ne. Sannan su sani gaba dayan aure ne ibada ba wai ibadar auren ba kadai, don haka bai kamata ba saboda matsalar da ta shafi ibadar aure kadai ace ana jin haushin juna ana takura ma juna da kalamai marasa kyau ko da mummunar zamantakewa. Yin haka ba zai kawo sauki ba sai dai ya kara dagula al’amura,
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe,
amin.