✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban neman aure (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili.  Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa a wannan fili.  Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan ladabi na biyar, shi ne zaben macen da ta dace; da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Yaya ake gane sace mai riko da addini?

Mu sani imani a zuciya yake, ba a iya gane mace mai addini daga ido kawai, ko daga yanayin shigarta ko mu’amalarta; domin da yawan mutane a wannan zamani suna nuna fuskokin riko da addini, amma inda za a yi kyakkyawan nazari, sai a tarar yanayin dabi’unsu sun yi nesa da koyarwar addini.

Don haka ba wai da ganin mace mai sa hijabi, yawan zuwa Islamiyya, tsare gida ko yawan jin kunya ne sai a ce an samu mai riko da addini ba. Dole sai an zurfafa bincike, an tabbatar cewa riko da addini ba a zahiri ba ne kadai, a’a, har a badini cikin zuciya, abin haka yake.

Za a yi irin wannan zuzzurfan bincike ne ta hanyar tambayar wadanda suka santa, suka zauna da ita kuma suka yi mu’amala da ita na tsawon lokaci, kamar kawayenta, makwabtan gidansu, malaman makarantarsu na da can da na yanzu, ’yan ajinsu a makaranta, ’yan uwanta na bangaren uwa da na uba da sauran duk wanda aka ga yana da muhimmanci a rayuwarta da zai iya bayar da wani bangare na yanayin halayyarta, dabi’unta da kuma mu’amalarta.

Sannan wajen yin irin wannan bincike dole sai an sa kulawa da taka-tsantsan; saboda yanayin gubacewar zamani. Da yawan mutane zukatansu dauda ta yi yawa;  wadansu za a iya tambayarsu su ki fadar gaskiyar da suka sani game da yarinyar da ake bincika, wadansu na yin shiru da nufin wai kada su fadi asalin halayenta marasa kyau su hana mata samun mijin aure. Wadansu suna yin haka da nufin hassada da kyashi kada su fadi kyawawan halinta auren ya yiwu, don haka sai su fadi halayen da take da rauni kadai, su ki fadar halayen kirkinta. Wadansu ma sukan zauna su shirya karairayi na muzantawa don dai su hana yiwuwar auren. Don haka maniyyacin aure sai ya sa lura da kiyayewa da irin wadannan mutane yayin da yake bincike, duk maganar da ya ji mai kyau ko mara kyau kada ya dauke ta a haka har sai ya kara bincikawa ta wata kafar daban ya tabbatar da ingancinsu kafin yin aiki da su.

Siffofin mace mai riko da addini:

Tauhidi: Abu na farko, kuma mafi muhimmanci da dukkan wata mace mai riko da addini ya kamata ta siffantu da shi shi ne  kyakykyawan Tauhidi, wanda ya kunshi kadaita Allah wajen bauta da kadaita Shi a cikin dukkan harkokin rayuwa na yau da kullum. Da kuma yin addini kamar yadda Annabi (SAW) da sahabbansa managarta suka yi ba tare da yin kari ko ragi ba. Lallai Tauhidi babban al’amari ne, abin dubawa da yin kyakykyawan nazari wajen zabar matar aure. Domin in Tauhidi ya samu rauni, to dukkan bangarorin addini gaba daya za su raunana. In kuma Tauhidi ya kafu da kyau a cikin zuciya, to zai tabbatar da kafuwar sauran bangarorin addini. Mu fahimci cewa ’ya mace, saboda yanayin raunin da ke tattare da halittarta, tana saurin samun rauni ta bangaren Tauhidi musamman ta hanyar amince wa wasu ayyuka masu raunata Tauhidi don samun saurin kawar da wata matsala ko damuwa da ta taso mata. Don haka sai a binciki yanayin halayya, nisan hankali da juriyar matar da za a nema da aure, da haka ne za a iya fahimtar ko za ta iya riko da tauhidinta komai tsanani, ko kuwa irin wadda da ta ji wata ’yar matsala irin ta halin rayuwa ta matso ta, za ta garzaya wajen boka ko malamin tsibbu da nufin samun warakar matsalarta. Don haka akwai hadari sosai a cikin auren macen da tauhidinta bai inganta ba; hasali ma, Allah (SWT) Ya fada cikin LittafinSa Mai girma cewa yin hakan haramun ne ga muminai:

“Mazinaci ba ya aure face mazinaciya ko mushirika, mazinaciya ba mai aurenta face mazinaci ko mushiriki; kuma an haramta wannan a kan muminai.” Suratun Nur; Aya ta 3.

Don haka dole maniyyacin aure ya dage ga neman mace mai tauhidi domin wannan alama ce gare shi cewa shi  mai tauhidi ne kuma ba mushiriki ba ne ba mazinaci ba ne.

Sai mako na gaba insha Allah.   Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.