✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Labarin banza ta kori wofi

Barka da warhaka Manyan GobeYaya karatu? Ina fata kuna mayar da hankali wajen bitar karatun da ake koya muku a makaranta. Kada ku rika wasa,…

Barka da warhaka Manyan Gobe
Yaya karatu? Ina fata kuna mayar da hankali wajen bitar karatun da ake koya muku a makaranta. Kada ku rika wasa, ko ku rika zuwa makaranta a makare. Kada ku rika jin kunyar yin tambaya idan har ba ku gane darasin da aka koya muku ba.
A wannan makon na taho muku da labarin Banza ta kori wofi. Ku bi labarin bi-da-bi don ku samu ribar darussan  da ke ciki. Ina fata za ku yi hutun karshen mako lafiya. Naku: Bashir Musa Liman

Labarin banza ta kori wofi

Wata rana wani mutum da ake kira Haro zai yi tafiya zuwa wani kauye da aka gayyace shi biki, sai ya je gidan wani mutum da ake kira Baso, wanda ke bayar da hayar jaki. Bayan Haro ya je gidan Baso ne ya yi sallama, Baso ya amsa sannan sai ya fito. Suka gaisa, daga baya sai Baso ya shaida wa Haro abin da ya kawo shi. A nan Baso ya ce ba zai ba shi hayar jaki ba. Wannan ya sanya Haro ya fusata, sannan ya yanke shawarar tafiya a kasa.
Yana cikin tafiya ne rana ta fito sosai, zafi ya karade ko’ina. kishin da yunwa suka dame shi, hakan ta sanya da ya je wani kauye sai ya huta, ya kuma nemi abinci ya ci. Ya kama hanyar ci gaba da tafiya ke nan, sai ya hadu da wani mai jaki a kan jakinsa. Bayan ya yi masa sallama ya amsa, sai Baso ya nemi mai jaki ya karbi kudi don ya hau jakin. A nan suka yi ciniki, kowa ya amince. Kana mai jaki da Haro suka hau jaki, sannan suka ci gaba da tafiya.
Suna cikin tafiya, sai mai jaki ya ce, ya kamata su huta, sai Baso ya ce allanbara sai dai su ci gaba da tafiya.
“Yanzu fa jakin ba naka ba ne, domin na biya ka.” Baso ya ce da mai jaki bayan ya kalle shi. “Haya ka dauka ba wai sayar maka na yi ba. Kuma shi ke nan don na bayar da shi haya, sai na bari a wahalar da shi?” Mai jaki ya mayar wa Baso amsa.
“karya kake yi, sai abin da na ga dama zan yi da jakin nan, domin ka riga ka karbi kudi.” Baso ya ce cikin karaji.
Wasa-wasa takaddama ta yi zafi a tsakaninsu har ta kai suka fara zage-zage. Ba su dauki lokaci a haka ba suka fara bai wa hammata-iska. Suna cikin bugi-in-buga ne sai jaki ya shiga gudu ba tare da sun lura ba. A karshe sun yi wa junansu lilis, jaki kuma ya gudu.  
Ina so Manyan Gobe su aiko da darasin da suka koya a dangane da wannan labarin. Sai na ji daga gare ku.

%d bloggers like this: