✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyautar sabulu ta sa Shata ya yi min waka – Bako Zuntu

Alhaji Bako Zuntu na  PZ, Alhaji Bako mai kayan masarufi ,Alhaji Bako ba bako ba ne a Zazzau, Zariya za ni in huta, in ishe Bako…

Alhaji  Bako Zuntu a zamanin daAlhaji Bako Zuntu na  PZ,
 Alhaji Bako mai kayan masarufi ,
Alhaji Bako ba bako ba ne a Zazzau,
Zariya za ni in huta, in ishe Bako Zuntu na PZ.

Cikin mutum 97 da marigayi Dokta Muhammadu Shata ya yi wa waka a Lardin Zazzau saura mutum hudu ke raye, daga cikinsu akwai fitaccen dan kasuwar nan Alhaji Bako Zuntu. Aminiya ta tattauna da shi inda ya ce kyautar sabulu ta sa Shata ya yi masa waka:

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Bako Zuntu: Assalamu alaikum, sunana Alhaji Usman Bako Zuntu Zariya, an haife ni a garin Zuntu da ke karamar Hukumar Kubau da ke Jihar Kaduna a 1939, a yanzu shekaruna sun kama 75 ke nan. Sunan mahaifina Malam Halliru, mutumin Kano ne kuma mahaifiyata Malama Hafsatu Bafulatana ce. Mahaifina ya rasu ina dan kimanin shekara bakwai da haihuwa, daga wannan lokacin na shiga matsaloli daban-daban na rayuwa wanda a dalilin haka ya sa na zauna da mutane da dama a matasayin iyaye, ta haka ne na samu na yi karatun allo a cikin wannan hali na rashin mahaifi har na kai matsayin saurayi a lokacin na kama kasuwanci inda a yau na shahara a kai.
Cikin harkokin da na yi a rayuwata na yi tela (dinki) na yi haya, na yi dillanci kuma na yi tallar kayan koli na yi tireda da kuma noma. Wadannan sana’o’in na yi su ne tun ina saurayi kuma a hannun iyayena, bayan na kawo karfi sai aka fitar da ni daga gandu daga nan sai na yi aure wanda daga cikin al’adun Hausawa mahaifinka ko marikinka shi ne ya kamata ya yi maka aure. To bayan nan na koyi hulda da jama’a yadda zan zauna da jama’a lafiya, a dalilin karatun addini da kuma yaki da jahilci da tarbiyyar da na samu a wajen magabatana da na zauna a hannusu kuma na shahara a kasuwanci na zagaye garuruwan Jos da Anacha da Legas da Maiduguri da Kano da sauran wurare da dama a harkar kasuwanci. Tun ina zaune a garin Zuntu nake wadannan yawace-yawace a inda daga bisani na dawo Zariya da zama. A 1984 jama’ar Zariya da kewaye lallai sun tabbatar da cewa Alhaji Usman Bako Zuntu dan kasuwa ne, domin a wannan lokacin kowa ya san irin wuya da matsaloli da aka samu na kayan masarufi, a wancan lokacin idan na samu kayan masarufi daga PZ  nakan sayar ne kai-tsaye ga jama’a domin amfanin talakawa.
A bisa kasuwanci da kuma abokan kasuwancina irin su Alhaji Lawal Mai Saurin Zuwa wanda shi ne abokin kasuwancina na farko da kuma Idi Rasdan wanda aka fi sani da Garba Edi dankoli. To bayan na dawo Zariya da zama sai na kara fadada harkokina ban dai bar noma ba, na kuma kara da harkar kwangila.To ka ji yadda al’amurana suka kasance.
Aminiya: Wace irin dangantaka ce a tsakaninka da marigayi Alhaji Mamman Shata har ya yi maka waka?
Bako Zuntu: Ai da mawaki da ’yan jarida wasu rukunai ne da ke saurin jin mutum da ya yi fice ko bajinta, musamman wanda ke taimaka wa jama’a don su yi hulda da shi.
Aminiya: A ina kuka hadu da Shata har ya yi maka waka?
Bako Zuntu: Mun hadu da Shata ne a lokacin da ya tafi kasar Amurka inda ya kwashe lokaci mai tsawo, a daidai wannan lokaci kayan masarufi suna wahalar samu, kuma su Alhaji Bako Zuntu ne ke da hanyar samowa da sayarwa ga jama’a, ta nan ne da wani yaron Alhaji mamman Shata a Sabuwar Unguwa Magume mai suna Ba-Ka Toshi, wanda yakan ziyarce ni a kowane lokaci, sai ya ce maigidansa ba ya nan ya tafi Amurka. Hajiya matar Shata ta aiko tana son sabulu, Ba-Ka Toshi ya je mata da shi sai na ce wa Ba-Ka Toshi ai kaya ya tsinke a gidin kaba, sai na ce ya yi hakuri sai bayan kwana biyu na dauki mota da sabulun wanka da na wanki katan-katan sai muka tafi Funtuwa muka kai wa iyalan Shata, inda Ba-Ka Toshi ya yi jagoranci muka isar da kayan ga iyalan Shata kafin ya dawo daga tafiyar da ya yi, Hajiya ta yi murna ta kuma sanya albarka. Bayan da Shata ya dawo daga tafiya sai ya ga sito cike da sabulu sai ya tambayi Hajiya wane ne ya shigo mini gida? Sai ta amsa masa cewa mai kayan masarufi Alhaji Bako Zuntu, sai Shata ya ce lallai zan nemi inda yake domin in yi masa godiya bisa wannan karamci da ya yi wa iyalina, wannan shi ne sanadiyyar haduwarmu da Alhaji Mamman Shata.
 Da Allah Ya kawo Mamman Shata birnin Zariya, sai Ba-Ka Toshi ya ce masa mutuminka wanda ya kai maka sabulu yana nan a gari, kada ka manta da shi domin wakar da za ka yi masa ne kawai za ta biya shi abin da ya yi maka, daga nan ne sai Alhaji Mamman Shata ya fara yi mini waka.
Aminiya: Bayan wannan lokacin kun ci gaba da mu’amala da Shata?
Bako Zuntu: To ka san Shata majnuni ne, shi ba maganar kudi yake yi ba, shi dai ya ga an saurare shi, mun ci gaba da harkoki da Mamman Shata har Allah Ya yi masa rasuwa.
Aminiya: Me za ka iya tunawa a huldar da kuka yi da Shata?
Bako Zuntu: Abin da zan iya tunawa da shi, kuma ya ba ni mamaki a wancan lokaci, ni mai arziki ne ba mai kudi ba, amma Shata bai taba yin bara ko neman wani abu daga gare ni ba, illa dai ya mayar da bikin da na yi masa a lokacin da ba ya Najeriya na alheri, domin ba maganar kudi ne ta hada ni da Shata ba.
Aminiya: Alhaji Bako daga cikin mutum 97 da Shata ya yi wa waka a Zariya yanzu haka ku hudu ne kuke raye, akwai Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da Alhaji Bashari Aminu Iyan Zazzau da Alhaji Mannir Jafaru Yariman Zazzau sai kuma kai dan kasuwa. Yaya kake jin irin yadda wakokin da suka ka gabata da kuma ku da kuka rage?
Bako Zuntu: Har kullum in na ji wakar Shata nakan gode wa Allah saboda mafi yawan wadanda ya yi wa waka sun rasu, shi ma Shata ya rasu, amma Alhaji Bako Zuntu yana nan kwance a daki yana sauraren basirar marigayi Shata. fatana Allah Ya sa mu cika da imani.
Aminiya: Ko kana da sako ga mawakan wannan zamani?
 Alhaji  Bako Zuntu a yanzuBako Zuntu: Su ci gaba da kokarin zakulo mutanen da suka bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma da kuma kasa baki daya, ta haka ne za a rika tunawa da zu bayan ransu kamar yadda ake tunawa da su marigayi Alhaji Mamman Shata.
Aminiya: Alhaji, maganar iyalai fa?
Bako Zuntu:  Ina da mata biyu da ’ya’ya 30, maza 16 da mata 14.