Wata mata a birnin Massachusetts da ke kasar Amurka da kyanwarta ta gudu daga gidanta ma bene uku ta taga ta sake hadewa da ita bayan shekara shida.
Kafar labarai ta UPI ta ruwaito a makon jiya cewa matar mai suna Margaret Kudzma ta ce kyanwarta mai suna Mini Mad, ta sulale ne daga gidanta da ke kasan garin Peabody ta taga a shekarar 2015.
- Talauci ya sa sojoji yin jigilar fasinja da jiragen yaki
- Hukumar Kwastam ta kama hauren dala miliyan 54 a Legas
Ta ce tun a wancan lokaci ta rika tallata bacewar a alluna da kafafen sadarwar zamani da jaridu a kokarinta na gano kyanwar.
Kudzma ta kare da kafa cibiyarta ta ceto marar neman riba da ta sanya wa suna The Rescue Business a shekarar 2016 lokacin da yunkurin gano kyanwa Mini Mad ya kai ta ga gano wani ayarin kyanwoyi jibge a wani wuri a makwabtanta.
Kudzma ta ce ta kadu a makon jiya lokacin da ta samu kiran waya daga Dokta Samantha Simonelli, wata likitan dabbobi a garin Wakefield, wadda ta ce ta ga bayananta a shafin microchip kan wata kyanwa da aka kai mata.
“Abin da na iya ji shi ne ‘ruwan kasa da fari’ nan take na ajiye tarho din,” Kudzma ta shaida wa jaridar Eagle-Tribune.
Kudzma ta samu labarin an gano kyanwarta Mini Mad ce a garin Rebere, inda wasu iyalai suka ciyar da ita na wasu watanni kafin daukarta zuwa gidansu.
Sun kai ta asibitin dabbobi ne lokacin da suka lura da wani rauni a kunnenta kuma a lokacin ne Simonelli ta gano wata alama da mai kyanwar ta sanya mata kuma ta bayar da bayani a kai a sanarwar da ta rika fitarwa bayan bacewar kyanwar.
Kudzama ta rubuta a shafinta na Facebook cewa, “Wani abin mamaki ya auku.
“Na gode wa duk wanda ya shiga cikin wannan aiki na bincikowa.”
Kudzma ta ce ta sa ana bincikar lafiyar Mini Mad sosai don tabbatar da ba ta tare da wani ciwo sakamakon tsallen da ta yi daga tagar benenta mai hawa uku.