✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta karrama limamin da ya tausasa kyanwa yana jan Sallah

Ya kayatar da jama’a da dama hatta wadanda ba Musulmi ba daga sassan duniya.

Gwamnatin Aljeriya ta karrama Imam Walid Mehsas wanda kyanwa ta dare jikinsa a daidai lokacin da yake jagorantar Sallar Tarawih.

Limamin cikin tausasawa ya yi ta shafar kwanyar wadda ta sumbaci kuncinsa kafin ta sauka daga jikinsa don radin kanta.

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ne ya nuna yadda Imam Walid ya mu’amalanci kwanyar cikin kyan yanayi, lamarin da ya kayatar da jama’a da dama hatta wadanda ba Musulmi ba daga sassan duniya.

Limamin ya sha yabo da jinjina, yayin da manyan kafafen yada labarai na duniya suka yi ta yada labarin.

Gwamnatin Aljeriya ta gayyace shi ta shirya masa liyafa ta musamman, inda Ministan Kula da Lamurran Addini na Kasar, Dokta Youssaf Belmahdi ya yaba masa kan wannan kyakkyawar dabi’ar da ya nuna wa dabba.

(rfi)