Wata kyanwa marar lafiya da aka kai asibitin dabbobi na Karolina ta Kudu a Amurka, tana can tana farfadowa bayan da likitocin dabbobi suka yi mata tiyata suka ciro kullallun gashi daga cikinta har guda 38.
kungiyar Kula da Dabbobi ta Charleston Animal Society ta ce wani mutum ne ya kai kyanwar mai suna Juliet asibitin inda ya ce ya gan ta an bar ta a wajen wani gida a lokacin da tsofaffin mazauna gidan suka bar jihar.
- Mun fara cire kananan yara daga rajistar zabe —INEC
- Yadda aka hallaka ’yan Boko Haram da sabbin sansanoninsu a Borno
Mutumin ya lura kyanwa Juliet tana ramewa kuma ba ta cin abinci na wasu kwanaki, inda bayan gwaji likitocin dabbobin aka gano wani abu ya cushe a cikin cikinta.
Daraktan asibitin dabbobin, Leigh Jamison, ya ce ayarin masu aikin tiyata sun kadu a lokacin da suka gano abin da ya cushe a cikin nata gasusuwa ne a kulle har guda 38.
“Ban taba ganin wani abu irin wannan ba,” Jamison ya fadi a wata sanarwar manema labarai.
Jamison ya ce yanzu kyanwa Juliet tana samun sauki kuma cushewar ta shafi kodarta sai da aka yi mata jinya.
“Muna kula wajen ba ta abinci, kuma muna aiki sosai don ganin ta dawo da koshin lafiyarta,” in ji Jamison.