Mai kyanwar da ta fi kiba da mutane da dama suke kira da ‘Kyanwa mafi kiba a duniya’ tana fuskantar tuhumar cin zarafin dabbobi kan yadda ta bar kyanwar ta yi kibad da ta wuce kima.
Kyanwar mai suna Lyznia, fitacciyar kyanwa ce mai kyan gani, wacce siffarta ta samu mabiya sama da dubu 10 a shafin Facebook cikin kankanin lokaci.
- Kyankyaso ya makale masa a kunne har kwana 3
- Za a fara daure ma’aikatan lafiya da na lantarkin da suka shiga yajin aiki shekara 5 a Sri Lanka
Wallafa hotunan kyanwar mai kiba ta sa sun rika yaduwa a Intanet, inda mai kyanwar ’yar kasar Rasha, ta fara shan suka a Intanet saboda ciyar da kyanwar fiye da kima da rashin damuwa da girman kyanwar a nan gaba.
Sai dai matar ta rika mayar da martani ga masu sukanta, inda ta ce Lyznia na fama da matsalar kiba tun lokacin da ta fara daukar ciki a ’yan shekarun da suka gabata.
“Akwai rashin fahimta. Don haka bari mu bayyana su a fili. Ba mu taba ciyar da Lyznia fiye da kima ba,” mai kyanwar ta wallafa a cikin wata sanarwa.
Ta ce, “Wadansu mutane sun rubuta cewa muna yin haka ne da gangan. Yaya kuke tunanin hakan? Har ma ta ki cin wani abinci sai abincinta. Gaskiya kyanwar tana da ciki kuma ta haihu, bayan ta haihu ta ci gaba da kiba, amma ba mu ce wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa ta kara kiba ba.”
Matar ta ci gaba da bayanin cewa, Lyznia ta yi kiba ne bayan da ta samu juna biyu na farko, kuma duk da yawan kai ta ga likitan dabbobi, ta ci gaba da kiba.
An rubuta wa kyanwar nau’o’in abinci iri-iri, amma ta ci gaba da kara yin nauyi har sai da aka fara ba ta gram 29 na abincin Royal Canin a kowane abinci.
“Da alama ta daina yin nauyi tare da shirinta na yanzu, amma har yanzu akwai matsaloli tare da ita na rama,” inji matar.
“Ba za mu iya kai ta ga likitan dabbobi kullum ba, amma tabbas za mu iya kai ta idan bukata ta taso,” inji ta.
Kodayake kwatanta hotuna na baya-bayan nan da wadanda aka wallafa lokacin da aka fara bude asusun Lyznia a shekarar 2020, ya nuna a zahiri kyanwar ta samu karin girma sosai, sai dai masu ita sun dage cewa har yanzu tana iya tafiya, tana iya yin wasa har ma ta yi farauta.
Duk da haka sun yarda cewa tana bukatar karin kwazo. Duk da wannan bayani, zargin cin zarafin dabbar ya ci gaba da fitowa daga masu sharhi, tare da zargin mai ita da yunkurin kashe Lyznia sannu a hankali.
Wani mai amfani da shafin Instagram ya yi tambaya cewa, “Me ya sa kika bar ta ta yi girma?” Wani kuma ya rubuta cewa, “Kyanwar za ta iya mutuwa a kowane lokaci.”
“A daina cin zarafin dabbobi, abin mamakin yadda aka ciyar da dabbar ana gab da kashe ta, don kawai ta zama kyakkyawar dabba, wadansu mutane ba su da cikakkiyar lafiya,” inji mutum na uku.
A yunkurin kwantar da hankali da fayyace abubuwa, mai Lyznia ta wallafa bidiyon yadda take ciyar da kyanwar da giram 29 na abinci, tare da fatar shawo kan “Wadanda ba su yarda ba,” cewa kyanwar tana cin abinci.
Lyznia na iya zama kyanwa mafi kiba a duniya a yanzu, kuma ita ce mafi kiba a tarihi. Wadda a baya lakabin na wani babban mazuru ne mai suna Tabby ne mai nauyin kilo 21.