Kushe halitta ga kowa abu ne mai sa bacin rai, musamman kasancewar galibi wanda aka yi wa ba shi da yadda zai yi da yadda Mahalicci Ya yi shi.
Abubuwa da dama kan sa al’umma kushe halittar wani, musamman idan ya fita daga sahun wadanda ake wa kallon masu kyawun siffa.
- An kashe Jagoran CAN da wasu mutum 5 a Kaduna
- Gudaji Kazaure: Ina nan tare da Buhari, duk da na bar APC
Siffofi da dama da ake alakantawa da kyau dai kowa na muradin samun su, wanda hakan ya sanya wadanda ba su da su ke kokawar nemowa ta karfi da yaji, ta hanyar shafe-shafen mayuka, ko allura, ko ma a wani lokacin tiyatar kwalliya.
To sai dai wadanda alamu suka nuna hakan ya fi damun su saboda kallon da ake musu na adon gari, su ne mata, wadanda da dama daga cikinsu yanzu suka tashi tsaye domin ganin sun fita daga jerin wadanda ake ganin ba kyawawan ba ne, ko kuma nuna bacin ransu kan hakan, musamman a kafafen sada zaumunta.
Kiba na daga jerin wadancan siffofin da ake ganin nakasu ne ga kyau.
Hakan kan sanya tun yarinta ake samun masu tsokanar wadanda ke da ita har zuwa girma, balle ma ace mace ce.
Wasu tun daga gida za su fara damun ta da ya fa kamata ta rage kiba saboda maza ba sa son mace mai kiba, kar ta rasa mijin aure, idan kuma mai auren ce, to kar a yi mata kishiya siririya, ta kwace mijin.
Wannan tsangwama ba ga iya abokan karatu ko gida ta tsaya ba, wani lokacin har a gurin aiki da ababen hawa na haya sukan fuskanci wannan tsangwama, in da ake ganin kibar tasu za ta kawo cikas ga gudanar da aikin ko wajen da za su cinye a motocin hayar.
Wannan ya sanya wasunsu suke shiga damuwa domin ta ko’ina ba sauki sai kalilan daga mutane wadanda su ma kan fito suna Allah wadai da wannan dabi’a ta kushe da wasu ke yi.
Dangane da haka mun tattauna da wasu mata da ke da kiba domin jin ko sun taba fuskantar irin wadannan maganganu ko dabi’a, da kuma halin da suke shiga idan hakan ta faru — sun kuma bayyana mana mabambatan ra’ayoyi kan haka.
Abin da matan ke cewa
Bilkisu Sulaiman da aka fi sani da Arewa Queen, shahararriya ce a kafafen sada zumunta da ba ta shakkar bayyana ra’ayiyinta kan al’amura daban-daban.
Mun kuma tattauna da ita inda ta bayyana mana cewa ba abu ne mai sauki ba rayuwa da kiba a wannan zamanin, musammna saboda bakin mutane, duk da ana sane da cewa halittarka ce ba ka da yadda za ka yi.
Amma hakan bai hana wani ya ci maka mutunci kanta, ba tare da sanin wasu na kokarin ragewa ba amma abin ya ci tura.
“Misali ko motar haya ka je hawa sai a ce kudin motar mutane biyu za ka biya saboda za ka ci wuri da yawa, kuma fa namiji ba a yi masa haka.
“Hakan gaskiya na sanya kamuwa da lururar damuwa ga wasu, ki ga mutum ya yi ta kadaice kansa, saboda gudun waccan kyamar.
“Kuma duk Turawa ne, sun saka mana dabi’ar cewa siririyar mace mai siririn wuya da siriryar kafa ita ce mai kyau”, in ji Arewa Queen.
Ta ce “Kwanaki kin ga akwai wa’azin wani malami da na ji yana cewa wai duk mace mai kiba ta yi duk yadda za ta yi ta rage don ba abu ne da ake so ba ga ’ya mace.
“Kin ga irin wannan ne yake sanyawa wasu su yi ta shaye-shayen abubuwan da za su saka su rage kiba har ya cutar musu da hanta ko wani abu a jikinsu, saboda su ma suna so su ji cewa ana yi da su a cikin al’umma,” in ji ta.
A hannu guda kuma mun tatatuna da wata fitacciyar ’yar jarida a Kano, Khadija Ishaq Bawas, inda ta ce ita ba ta taba fuskantar wannan matsalar ba tun daga yarinta, kasancewar ko a makarantar da take ba ita kadai ce mai kiba ba, haka ma kuma a gida.
“Kinga ko a bangaren kayan sakawa ban taba fuskantar wannan matsalar ba, saboda ni kaina mai dinki ce wani lokacin ma a gurina za a ga wani samfirin dinkin a ce za a yi irinsa, kuma ko na gani ana yi wa wasu baya damu na,” in ji ta.
Ta ci gaba da cewa ba gaskiya ba ne a ce wai kiba na hana samun masoyi, domin zan iya kirga miki adadin lokutan da na fita ban samu wanda ya min tayin soyayya ba, har ta kai ta kawo ma yanzu a kafafen sada zumunta ba na amsa sakon wanda ban sani ba, saboda na san karshen zancen”, in ji ta.
Daga Jihar Kaduna ma Aminiya ta tattauna da wata fitacciyar ’yar jaridar mai suna Zahra Musa, inda ta bayyana mana cewa takan ji bacin rai da zarar wani ya tsokane ta kan kibarta, ko ya fara surutu a kan ya kamata ta rage kiba, duk da ita kalau take, hasali ma kibarta ba ta yi shaharar da za a daga mata hankali ba.
“Gaskiya duk bacin ran da na ji ba na bari ya dame ni tsawon lokaci saboda na san illar da damuwa ke jefa mutane.
“Mata da yawa sun fada cikin kunci da kadaice kai saboda tsangwamar da suke fuskanta, amma gaskiya ni ban ga abin surutu a kan haka ba, domin wasu ma sun yi duk kokarin da za su yi su ragu, idan hakan ba ta samu ba sai su shiga cikin tsananin damuwa.”
Illar hakan a mahangar Manzarta Halayya Dan Adam
Mun tattauna da Manzarci kan Halayyar Dan Adam da ke koyarwa a Jami’ar Tarayya ta Gusau a jihar Zamfara, Dokta Abubakar Sadiq Haruna, ya kuma ce abubuwa da dama na sanya tun daga kuruciya zuwa girma tsangwamar ta shiga zuciyar wasu, har ta haddasa musu illoli irin su cutar tsananin damuwa, da rashin kwarin guiwar gudanar da abubuwan walwala ko ci gabansu.
Malamin ya kuma ce wannan na kawo nakasu sosai ga rayuwarsu tun daga wannan lokaci har girmansu, domin girman jikinsu zai iya sanywa a dinga ba su abubuwan da shekarunsu ba su kai su yi ba, amma saboda girman jikinsu, sai a rika ba su shekarun da suka fi karfinsu.
Haka zalika tsokanar da ake wa mata tun yarinta, na sanyawa ta rasa kawaye saboda gudun tsangwamam, haka kuma wuraren wasa ma da sa’o’inta ke zuwa zai gagare ta ko a makaranta, saboda watakila fada mata ta yi girma da yin abubuwan da sa’o’inta ke yi.
“Ni kaina ina da da yake da kiba da aka dinga ba shi aikin da ya fi karfin shekarunsa a makaranta, har sai da na je na yi musu bayani, saboda su daina ba shi abin da ya fi karfin shekarunsa”, in ji shi.
“Ba a iya nan tsangwamar ta tsaya ba, ko a bangaren sufuri musamman na jirgin sama da na kasa, za ki ga idan mutum na da kiba sosai, kudin da zai biya na musamman ne, domin za a fada masa cewa akwai iya nauyin da jirgin ke dauka, don haka in dai ya na son hawa kamar kowa sai ya kara kudi”, in ji Dokta.
Haka kuma ya ce a kasashen da aka ci gaba irin wadannan masu kibar tanadar musu aji na musamman ake yi, ko kuma a sami mai zuwa gida ya koyar da su, saboda a kauce wa waccan matsalar.
“Hakan na sanya wasu su bar zuwa makaranta tun ba a je ko’ina ba, ko su tsane ta, saboda fargabar da suke ciki, wasu kuma sai ma an hada da ganin likitan kwakwalwa da saita tunani”, in ji Dokta Sadiq.
Ina Mafita?
Dokta Abubakar ya ce ya kamata iyaye su dinga lura tun yaro na karami su sanya ido kan halin da yake ciki da karfafa mishi guiwa kan takaita barin wannan tsangwama ta shiga jikinsua har ya kai ga shiga damuwa.
“Ba iyaye kadai ba, gwamnati ma ya kamata ta tanadar musu wuraren kiwon lafiya da ya dace da su, da kuma likitocin kwakwalwa har ma da na tunani, domin kula da bukatunsu.
“Haka kuma a tsara makarantu daidai da yadda su ma za su yi walwala kamar kowanne dalibi, domin su ma su ji cewa al’umma na damawa da su”.
“Ya kamata ma a tanadar musu da aji na musamman, saboda mutane ne da ke cikin yanayi mai bukatar kulawa, don haka ba su aji na musamman zai taimaka wajen rage musu damuwa, domin zai zama suna tare ne da mutane irinsu, in ji shi