✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwatsam ta kama kwantaina cike da makamai

An yi fasa-kwaurin makaman tare da kwantainoni tara na miyagun kwayoyi daga kasar waje zuwa Najeriya

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama kwantaina cike da makamai a Tashar Jiragen Ruwa ta Nome a Jihar Ribas.

Hukumar ta kuma kama karin wasu kwantainoni tara da ke dauke da muguwar kwayar Kodin.

Da yake nake kolin makamai da miyagun kwayoyin da aka kama a ranar Litinin, Kwanturolan Kwastam na Jihar Ribas, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce an shigo da makaman  Najeriya ne daga kasar Turkiyya.

Ya bayyana cewa masu fasa kwarin kayan sun sun boye su ne a cikin dilolin kayan gwanjo.