Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Ogun ta kama buhunan shinkafar ƙasashen waje guda 2,169 kowacce mai nauyin kilogiram 50, waɗanda aka yi safararsu ta ɓarauniyar hanya.
Da kuma wasu kayayyaki da darajarsu ta kai za a biya musu kuɗin shiga na hukumar Naira miliyan N229,112,424.00.
Sauran abubuwan da aka kama sun haɗa da tarin ɗaurin tabar wiwi 1,128, masu nauyin kilogiram 1,109.3kg, tare da dilar kaya 21 da buhunan 2 na tufafin da aka yi amfani da su da tayoyin mota 166 da kuma kwalaye 4,360 na takalman da aka shigo da su.
- Turmutsutsu: ’Yan sanda sun kama wasu bayan mutuwar yara 35 a Ibadan
- Mutum ɗaya ya mutu 4 sun jikkata bayan fashewar bam a Neja
Kazalika, Kwastan ta kuma kama man fetur 250 mai nauyin lita 25 kowanne, da motoci guda 20 da ake amfani da su na jigilar kayayyaki da kuma guda da aka yi amfani da ita a ƙasashen waje, samfurin Toyota Highlander 2012 duk jami’an kwastam sun kama su.
Shugaban riƙo na yankin, Mohammed Salisu Shuaibu, ya bayyana hakan a taron manema labarai na farko da ya gudanar a hedikwatar rundunar da ke Idiroko, jihar Ogun.
Shu’aibu, wanda ya karɓi ragamar shugabancin rundunar a kwanakin baya, ya ce an kama kayan ne a ‘yan kwanakin nan a wasu muhimman wurare da suka haɗa da yankunan Idiroko da Ilaro da Alamal-Rounda da yankin Obada Oko zuwa Abeokuta da Abule Kazeem zuwa Abeokuta da yankin Imeko zuwa Afon.
Ya bayyana wuraren a matsayin sanannen wuraren fasa kwabri.”
Shugaban yankin ya ce, “Jami’anmu na ci gaba da jajircewa wajen wargaza hanyoyin fasa kwabri da ke durƙusar da tattalin arzikinmu da jefa rayuka cikin haɗari da kuma kawo cikas ga masana’antun cikin gida.