✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama kayan miliyan 23.1 a Kebbi

Hukumar ta ce za ta ci gaba da yaki da masu yin fasa kwauri a jihar

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa (Kwastam) a Jihar Kebbi, ta ce ta kama haramtattun kayan Naira miliyan 23.1 tare da samar da kudaden shiga har Naira miliyan 144.8 a kan iyakar Kamba a watan Maris.

Shugaban hukumar a Jihar, Mista Ben Oramalugo ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zanta wa da manema labarai kan ayyukan hukumar na watan Maris a Birnin Kebbi a ranar Talata.

Ya ce kudaden shigar da aka samu, ya karu da kashi 164 cikin 100 na abin da ake sa rai a duk wata duk da zaben da ya shafi yawan shigo da kayayyaki cikin kasar.

“Bayan jerin tarurrukan da muka yi da kuma yin alaka da duk masu ruwa da tsaki da nufin dakile matsalar fasa-kwauri da karuwar kudaden shiga, mun samu gagarumar nasara a fannin samun kudaden shiga.

“Muna da fatan samun karuwa, mu haura abin da muka samu zhwa Naira biliyan 1.06 a shekara,” in ji shi.

Oramalugo, ya ce hukumar ta samar da hanyoyin da za a bi wajen tunkarar babban kalubalen da masu ruwa da tsaki na biyan haraji daga kasashe makwabta suke fuskanta a kan iyakar Kamba.

“A yanzu mun kama lita 16.375 na man fetur, katan 210 na taliyar kasar waje, dila 34 na kayan gwanjo da katan 109 na kayan abinci da sauransu.

“Kudirin harajin kayayyakin da aka kama ya kai Naira miliyan 23.1,” in ji shi.

Sai dai ya gargadi duk masu fasa kwauri da masu taimaka musu a jihar da su daina aikata munanan ayyukan da suke yi.

“Ba za mu nade hannanmu mu bar mutane suke yin abin da suka ga dama ba.

“Gwamnati na biyan makudan kudade don bai wa ‘yan kasa tallafin kayayyakin da ake shigo da su.

“Muna ci gaba da jajircewa wajen dakile ayyukansu na haram saboda muna da kayan aiki da dabaru kuma zamu himmatu wajen dakile duk ayyukansu,” in ji Oramalugo.