Hukumar Kwastam ta Kasa ta bayar da sanarwar sake bude iyakokin Jibiya da ke Jihar Katsina da ya sada Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Wannan sanarwa na cikin takardar da hukumar ta tura wa jami’anta da ke kula da iyakokin, dauke da kwanan watan 22 ga watan Afrilun da muke ciki.
Hukumar ta ce an sake bude kan iyakar ta Jibiya ne tare da sauran iyakoki na Idiroko da ke Jihar Ogun, Kamba a Jihar Kebbi da kuma Ikom da ke Jihar Kurso Riba.
Babban Mataimakin Shuganan Hukumar na Kasa (EI&I), DCGC El Edorhe, shi ne ya sanya wa takardar hannu hannu a madadin Kwanturola Janar na hukumar, Kanar Hamid Ali.
DCGC El Edorhe ya ce sake bude wadannan iyakoki na daga cikin umarnin Shugaban Kasa na ranar 16 ga watan Disambar 2020 inda aka bude iyakokin Babban Mutum, Seme, Illela da kuma Maigatari.