Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’yyar PDP.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da tsohon gwamnan ya sanya wa hannu a ranar Talata.
- Yamuna Aminu Kani: Abar koyi a harkar kiwon lafiya
- Matsalar tsaro: Kamfanin jiragen saman Azman ya dakatar da jigila a Kaduna
Idan ba a manta ba, Sanata Kwankwaso ya jima yana shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar, tun bayan kafa tafiyar siyasa ta TNM.
A ranar Lahadi ce, daya daga cikin jagororin darikar Kwankwasiyya kuma na gaban goshin Kwankwaso, Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida-gida), ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP, mai alamar kayan marmari.
Abba Gida-gida dai ya zargi jam’iyyar PDP da gaza bai wa bangaren na Kwankwasiyya dama, duk da irin halarcin da su kai wa jam’iyyar a zaben 2019.
Ana sa ran Kwankwaso zai tsaya takarar Shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar NNPP, a babban zaben 2023 da ke karatowa.