✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ya faranta wa Kano Pillars rai

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a karshen makon jiya ne ta faranwa wa ’yan kwallon Kano Pillars rai bayan ta ware…

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a karshen makon jiya ne ta faranwa wa ’yan kwallon Kano Pillars rai bayan ta ware zunzurutun Naira miliyan 52 da dubu 500 don biyan albashin watan Afrilun wannan shekara da kuma na watanni biyu da ba a biya ‘yan kwallon ba.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Dokta Omar Faruk ne ya sanar da haka a ranar Larabar makon jiya a lokacin da yake hira da menama labarai jim kadan bayan an kammala taron majalisar zartarwar jihar na mako-mako.
&nbsp Kwamishinan ya ce za a biya daukacin ’yan kwallon da kuma jami’an da ke horar da su basussukan ne don a karfafa musu gwiwar cigaba da nuna kwazo a wasannin da suke yi.