Wani makusancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai suna Alhaji Aminu Abubakar Dabo ya karyata rade-radin da ake yada wa mai tsohon Gwamnan Jihar Kanon ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki.
Aminu Dabo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce lallai Kwankwanso na nan a Jam’iyyar APC, kuma rade-radin da ake yada wa kanzon kurege ne kawai.
“Tarukan da muke ta yi ba wani abu e face irin taruka da kowane dan siyasa ke yi. Amma ko kadan tarukanmu bai da alaka da canja sheka,” inji shi.