✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso da APC na musayar yawu kan rabon tallafin kayan abinci a Kano

NNPP na da hannu a badakalar da ta shafi karkatar da kayan abinci.

Jam’iyyar adawa ta APC a Jihar Kano ta mayar da martani ga jagoran Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, biyo bayan sukar Gwamnatin Tarayya da ya yi kan tallafin kayan abinci ga jihar.

A wani sako da Kwankwaso, ya wallafa a Facebook, ya yi Allah-wadai da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na shigar da ’ya’yan Jam’iyyar APC wajen rabon kason da jihar ta samu, inda ya bayyana hakan da cewa, cin amana ce ga dimokuradiyya.

Ya ce, yayin da sauran jihohi 35 ke gudanar da abubuwan da suka samu domin jin dadin al’ummarsu a hannun gwamnoninsu, amma a nan Jihar Kano, sai jigajigan Jam’iyyar APC ne suka gudanar da rabon kayan tallafi.

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya kare matakin na Gwamnatin Tarayya, inda ya bayyana cewa, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bai gamsu da yadda gwamnatin jihar karkashin jagorancin Jam’iyyar NNPP ta gudanar da rabon kayan jinkai da aka yi a baya ba.

Alhaji Abbas ya ce, ‘‘Shugaba Tinubu ya kuduri aniyar rage yunwa a kasar nan, amma gwamnatin Jam’iyyar NNPP a Kano na kawo cikas ga wannan yunkurin,’’in ji shi.

Ya zargi Gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da karkatar da tallafin da aka bayar domin talakawa da marasa galihu, wanda hakan ke bata aniyar Gwamnatin Tarayya.

Abbas ya kuma yi zargin cewa, wasu jami’an Jam’iyyar NNPP na da hannu a badakalar da ta shafi karkatar da kayan abinci.

Alhaji Abbas ya bukaci Kwankwaso da ya yi kira ga “shafaffen gwamnansa” da ya binciki wadannan abubuwa na rashin da’a da aka aikata.

Ya kuma jaddada cewa, Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin da mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya jagoranta, domin sa ido kan yadda za a raba kayan abinci a Kano, tare da mambobin jam’iyyun APC da NNPP da PDP da shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da gaskiya.

Da yake magana kan batun sauya Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS a Kano kwanan nan, Abbas ya ce matakin na daga cikin kudirin Shugaba Tinubu na ganin cewa,“shugabannin hukumomin tsaro masu himma” ne kawai aka tura jihar.

Ya kara da cewa, a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na wa’adi biyu, Kano ta kasance cikin kwanciyar hankali, ba a samu tashin hankali ba.

Ya ci gaba da cewa, rashin zaman lafiya a Kano ya samo asali ne daga ayyukan Gwamnatin Jam’iyyar NNPP.

Domin sun karfafa wa kungiyoyin matasa masu ta da hankali, musamman a lokacin zabe na 2023.