Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ce nan ba da jimawa ba za ta ci gaba da yin rijistar katin zabe wanda ta dakatar a watannin baya saboda annobar COVID-19.
Kwamishinan hukumar a Jihar Kogi, Farfesa James Apam shi ne ya sanar da hakan a garin Onyadega na Karamar Hukumar Ibaji ta Jihar Kogi.
James wanda ke jawabi ga masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen zaben cike gurbin da za a yi a karamar hukumar ya ta’allaka tsaikon yin rajistar a yankin a kan annobar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa zuwa farkon shekara mai zuwa za ci gaba da rajistar tare da kira ga wadanda ba za su samu damar kada kuri’a a zaben ba da su yi hakuri.
Ya ce zaben cike gurbin ya biyo bayan mutuwar dan majalisar da ke wakiltar yankin a Majalisar Dokokin jihar, Mista John Abah a watan Yuni.
Kwamishinan ya kuma ce INEC za ta samar da sinadaran tsaftace hannu, na’urar gwajin zafin jiki da kuma kiyaye sauran ka’idojin kariyar cutar.