A yau 6 ga watan Satumba, 2023 Bola Ahmed Tinubu ya cika kwana 100 a kan karagar mulkin a matsayin zabebben shugaban kasar Najeriya na 7 kuma shugaba na 16 tun bayan samun ’yancin kasar a 1960.
Ga kadan daga cikinsu a takaice:
Cire tallafin mai
Ranar 29 ga watan Mayu, 2023 da aka rantsar da Tinubu ya sanar cewa tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ke biya ya zama tarihi.
Tun a ranar farashin man ya fara tashin gwauron zabo, har ya ninninku daga N197 zuwa N620, wanda ya yi sanadin hauhawar farashin kaya da matsin rayuwa a tsakanin ’yan Najeriya.
Watsi da canjin Naira
A ranar ce kuma ya jingine wa’adin dokar canjin Naira da takaita cirar tsabar kudi da gwamnatin magabacinsa, Muhammadu Buhari, ta yi, wanda tun kafin zaben Tinubu, shi da ’yan Najeriya suka rika caccaka da zargin dokar da jefa jama’a cikin kunci, duk da cewa gwamnatin baya ta ce ta yi ne domin hana sayen kuri’u da kuma takura wa barayin dukiyar kasa.
Kasuwar canji
Tinubu ya janye hannun gwamnati daga kayyade farashin canji da nufin farfado da darajar Naira ta yi gogayya da kudaden kasashen waje.
Amma haka ba ta cim-ma ruwa ba, inda Dala ta yi ta hauhawa, har ta kai kimanin Naira 1,000, kafin daga baya ta fadi da kusan Naira 200, sannan ta sake yin sama.
Rikicin DSS da EFCC
A ranar da shugaban kasa ya shiga ofis aka wayi gari da takaddama tsakanin hukumar EFCC da DSS kan harbar ofishin da hukumomin biyu ke amfani da shi a Jihar Legas, lamarin da ya kai sai da ya taka wa DSS burki da cewa ta kyale EFCC, ya kuma yi gargadi cewa ba zai lamunci rikici tsakanin hukumomin tsaro ba.
Korar manyan hafsoshin tsaro
Hawan Tinubu babu jimawa ya sallami manyan hafsoshin tsaro ya nada sabbi, sannan ya hore su da su magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
Kafin nada su ya yi wa magabatansu alkawarin biyan bukatun rundunar tsaro da nufin dorawa a bisa nasarorin da gwamnatin da ya gada ta samu ta fuskar tsaro.
Boren NLC kan cire tallafi
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi zanga-zangar adawa da cire tallafin mai da ya jefa ’yan kasar cikin matsi.
Tana shirin shiga yajin aiki gwamanti ta lallashe ta ta janye.
Ranar 5 ga watan Satumba, kungiyar ta fara yajin aikin gargadi, bayan ta kaurace wa zama na biyu na sulhun da gwamantin ta kira.
Dakatar da Gwamnan CBN
Kwanaki kadan da fara aikin Tinubu ya sallami Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, wanda daga bisani hukumar tsaro ta DSS ta tsare kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Daga baya ta janye tuhumar ta sake gurfanar da shi kan wasu zarge-zarge 20 kan badakalar biliyoyin Naira, wanda har yanzu ake shari’a a kai.
Damben DSS da hukumar gidan yari
Bayan DSS ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu ne alkali ya ba da belinsa, amma ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari har sai ya cika sharuddan belin.
Sai dai kafin jami’an hukumar gidan yari su kai ga tafiya da shi jami’an DSS suka murkushe su a harabar kotu suka yi awon gaba, wanda hakan ya ja musu caccaka, daga bisani hukumar ta nesanta kanta da abin da jami’anta suka yi.
An kashe sojoji 36 a Neja
Rundunar Sojin Najeriya ta girgiza da mutuwar dakarunta 36 a yayin yaki da ’yan ta’adda da suka yi musu kwanton bauna a Jihar Neja.
Daga cikin sojojin akwai wasu 14 da suka kwanta dama a hatsarin jirgin soji a jihar.
An binne su bayan an yi musu jana’izar soji a Babbar Makabartar Sojoji ta Kasa da ke Abuja.
Nadin ministoci
A cikin kasa da kwana 100 Tinubu ya kafa tarihin zama shugaban da gwamnatinsa ta fi kowacce yawan ministoci da mutum 48, inda a karon farko ya nada ministoci biyu a ma’aikatar tsaro tare da kirkiro sabbin ma’aikatu.
Nadin tsohon Gwaman Jihar Ribas Nyesom Wike na jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar ministocin Tinubu ya ba da mamaki, kamar yadda aka yi ta mamakin musabbabin rashin tantance tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda daga bisani ya ce a kai mukamin ministan kasuwa.
Soke sayar da filayen jirgi
Tinubu ya kuma soke cefanar da filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari, matakin da ministansa na sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya sanar bayan Majalisar Dattawa ta umarci ma’aikatar da yin haka.
Bincikar shugaban EFCC
Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) Abdulrasheed Bawa yana daga cikin wadanda Tinubu ya dakatar kafin cikarsa kwana 100 a bisa mulki.
Sama da wata biyu Bawa na tsare a hannun hukumar DSS, ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.
Tallafin cire ‘subsidy’
Bayan cire tallafin mai Tinubu ya bullo da tsarin ba wa talakawa tallafin rage musu radadi na tsawon wata shida.
A watan Agusta ya ba wa kowace gwamnatin jiha kason farko na tallafin Naira biliyan biyar da ya hada da tsabar kudi da kuma kayan abinci domin su raba wa mutane a jihohinsu.
Shirin ba wa dalibai rancen kudi
Tinubu ya sanar da tsarin ba wa daliban manyan makarantu rance da za su biya bayan kammala karatu.
Sai dai har zuwa lokacin da gwamnatinsa ta cika kwana 100 a ofis, ba ta fayyace tanade-tanaden tsarin ba, duk da cewa ta yi alkawarin fara aiwatar da shi a sabuwar shekarar karatu da ke farawa a watan Satumba.
Yi wa jakadu kiranye
A lokaci guda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi wa daukacin jakadun kasar da ke kasashen waje kiranye tare da sanar da cewa wa’dinsu zai kare a ranar 1 ga wata Oktoba.
Wannan kusan shi ne karon farko da aka ga zababbiyar gwamnati ta yi haka a Najeriya.
Takaddamar juyin mulkin Nijar
Tinubu ya zama shugaban kungiyar ECOWAS, inda baya nan sojoji suka yi wa Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, juyin mulki, wanda Tinubu ya yi uwa, ya yi makarbiya na ganin an dawo da shi kan kujerarsa.
A kan haka ne ya ce kungiyar za ta dauki dukkan matakan da suka dace na dawo da mulkin dimokuradiyya a Nijar ko da ta hanyar karfin soji ne, furuci, matakin da majalisar dokokin Najeriya da wasu ke gani a matsayin neman hura wutar yaki a Nijar ko ma tsakaninta da Najeriya.
Da haka ya jagoranci kakaba wa gwamnatin sojin Nijar takunkumi, Najeriya ta katse wutar lantarki da take ba kasar, tare kafa rundunar ko-ta-kwana ta ECOEWAS da ke barazanar far wa gwamnatin sojin Nijar.
Daga bisani ya yi ta tura malaman addini daga Najeriya suka samu tattaunawa da masu juyin mulkin kafin daga bisani sojojin na Nijar da suka yi shirin yaki suka bude kofar tattaunawa da ECOWAS.