Kwamishinan Noma na Jihar Sakkwato, Muhammad Arzika Tureta, ya rasu da safiyar Litinin.
Arzika wanda shi ne tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Sakkawto ya rasu yana da shekara 62, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo bayan fama da rashin lafiya.
- An kori hadimin Dan Majalisa saboda Shekau
- Mahara sun kashe 3, sun tashi kauyuka 8 a Sakkwato
- Jana’izar Janar Attahiru: Yadda Gwamnoni suka fusata ’yan Najeriya
Muhammad Arzika, shi ne mutum na hudu a cikin Kwamishinonin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da suka rasu.
Sauran su ne Kwamishinan Kasa da Gidaje, Jeli Abubaka III; Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Surajo Gatawa; sai Kwamishinan Sadarwar Zamani, Nasiru Zarumai.
A baya Arzika ya rike mukamin Kwamishinan Ilimi a zamanin Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko.
Ya kasance dan Majalisar Jihar Sakkwato a karkashin rusasshiyar jam’iyyar NRC kuma tsohon dan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar mazabar Bodinga/Dange-Shuni/Tureta a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai da jikoki da dama.