Kwamishinan Ayyuka na jihar Anambra wanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a ranar Larabar da ta gabata, Injiniya Emeka Ezenwanne ya kubuta.
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba ne dai suka kutsa kai cikin wurin wani taro tsakanin dan takarar jam’iyyar APGA a zaben Gwamnan jihar, Farfesa Charles Soludo da wasu matasa a garin Isuofia dake Karamar Hukumar Aguta a jihar ta Anambra sannan suka yi awon gaba da shi.
- Yadda aka yi bikin daukar gawar Fir’aunoni a Masar
- COVID-19: Mutum 7 sun mutu bayan karbar rigakafin AstraZeneca a Birtaniya
Kazalika, ’yan bindigar wadanda ke dauke da muggan makamai sun kuma kashe jami’an ’yan sanda uku dake gadin Farfesa Soludo, sannan suka tafi da Kwamishinan lokacin da yake kokarin haura Katanga domin tsira daga gare su.
Wata majiya dake da kusanci da Kwamishinan ce ta tabbatar da kubutarsa inda ta ce yana cikin koshin lafiya.
A cewar majiyar, ko sisin kwabo ba a biya ba kafin a sami damar kubutar da shi, kuma ta ce wadanda suka sace shin ba su musguna masa ba.
Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin Ru ndunar ’Yan Sanda na jihar, DSP Ikenga Tochukwu ya ce Mista Emeka ya dawo gida cikin koshin lafiya bayan matsin-lambar jami’ansu ga ’yan bindigar har suka sake shi a dole.
Kakakin ya ce Kwamshinan ya dawo gidansa ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, hudu ga watan Afrilun 2021.