Wasu ’yan bindiga guda shida karkashin jagorancin shugabansu, Auwalu Daudawa sun mika wuya tare da sallama wa gwamnatin Jihar Zamfara bindigogi 28 kirar AK-47 a ranar Litinin.
Kimanin kwanaki goma da suka gabata ne wasu ’yan bindiga shida suka tuba tare da mika wa hukumomin Jihar bindigogi 14 suna masu alkawarin watsar da ayyukan ’yan bindiga da sauran ababe na ta’ada.
- An cafke mutane 3 masu dillacin makamai a Kebbi
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
- Kwastam ta kama kasusuwan zaki da hauren giwa na N1bn
Wadanda aka karbi tubansu a fadar Gwamnatin Jihar da ke birnin Gusau, sun yi rantsuwa da Alkur’ani cewa ba za su sake komawa wannan mummunar ta’ada ba.
Kazalika, jagoransu Auwalu Daudawa ya yi alkawarin janyo ra’ayin wadanda har yanzu suke rike da makamai domin su tuba.
Da yake karbar mutanen da suka tuba, Gwamna Bello Matawalle ya kirayi dukkan ’yan bindigar da su fito su amince da tsarin sulhu da gwamnatinsa ta kirkiro inda ya yi alkawarin kula da duk wadanda suka tuba.
“Gwamnatina za ta kula da duk ’yan bindigar da suka tuba sannan zan ci gaba da tattaunawa da su domin kawo karshen ta’addanci a Jihar,” in ji Matawalle.
Matawalle ya yi kira ga mutanen jihar, musaman ’yan siyasa da su bai wa gwamnatinsa goyon baya a kokarinta na kawar da masu satar mutane da sauran ababe na ta’ada.