✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kafanchan ta yaye dalibai

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (FSTC) da ke Kafanchan a Jihar Kaduna ta yi bikin yaye daliban da suka kammala karatu sakandare na bana.…

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (FSTC) da ke Kafanchan a Jihar Kaduna ta yi bikin yaye daliban da suka kammala karatu sakandare na bana.

Bikin wanda aka gudanar a harabar kwalejin a ranar Juma’ar da ta gabata ya samu halartar dalibai da malamai da sauran jama’a.

A kasidar babban mai jawabi a wajen taron, Mista Jesse Dakat ya yi kira ga daliban da suka kammala karatunsu su mayar da hankali wajen koyon sana’o’in da za su dogara da su domin sun samu halin ci gaba da makaranta ko ba su samu ba domin yawancin iyaye da kyar suke iya daukar nauyin karatun ’ya’yansu a matakin sakandare ballantana na gaba da ita.

Ya ce, “Ina kira gare ku da ku kawar da kanku daga tunanin sai kun yi aikin gwamnati. Ku yi amfani da ilimin da kuka samu a sakandare kada ku raina kanku domin ko mutumin da ya kirkiro mota (Henry Ford) bai yi karatun jami’a ba. A wannan marhalar da ake ciki na karayar tattalin arziki ku fara tunanin me za ku yi da zai amfanar da ku da al’ummarku domin babu al’ummar da ta taba samun ci gaba ta hanyar dogaro da gwamnati. Da yawa daga cikin wadanda suka tsaya jiran aikin gwamnati rayuwarsu na karewa ne a yawace-yawace a kan titi da shaye-shaye.”

Sai ya yi kira ga Hukumar Ilimi ta kasa ta samar da kayayyakin koyarwa na zamani tare da yi wa  malamai bita kan sababbin dabarun koyarwa don samun saukin koyarwa.

Tun farko jawabin Shugabar Kwalejin, Misis E.B Bamgbala ta bayyana nasarorin da makarantar ta samu a lokacin shugabancinta na shekara uku da suka hada da sanya wuta mai aiki da hasken rana da gina makewayi a wajen kwanan dalibai mata da karin wasu ajujuwa a makarantar. Sai dai ta koka kan wasu matsaloli da suke addabar makarantar da suka hada da karancin malamai da rashin biyan kudin makaranta a kan lokaci da karancin ajujuwa.

A wani labarin, kungiyar dalibai Musulmi (MSSN) ta Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Je-Ka-Ka-Dawo (GDSS) da ke Kafanchan ta gudanar da walimar kammala karatu tare da gabatar da sababbin shugabannin kungiyar.

Bikin, wanda ya gudana a dakin taro na Makarantar Sakandaren Raga, ya samu halartar iyaye da malaman makarantu da dama.

A jawabin Malam Abubakar Sadik dahir, ya yi kira ga dalibai mata su zamo masu kunya a duk inda suke domin kunya daga imani take kuma kowace al’umma tana kaunar masu kunya a cikinta. Ya yi kira su rika sanya tufafi na mutunci domin tsare mutuncinsu da na addininsu a duk inda suka tsinci kansu.

An raba satifiket ga tsofaffin shugabannin dalibai da kuma rantsar da sababbin shugabannin da suka karbi ragamar shugabancin daga gare su.