✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalejin Kaduna: Iyaye da dalibai sun yi zanga-zanga

Iyayen daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya na zargin gwamnati na rashin damuwa da sace daliban.

Iyaye da daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya, Afaka, da ke Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zangar lumana kan gazawar gwamnatin jihar na ceto dalibai 39 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar.

Iyaye da daliban kwalejin sun hallara a harabar makarantar ne tun guabanin Azahar don yin kira ga mahukuntar jihar wajen ceto daliban da aka sace ranar Alhamis da dare.

Masu garkuwa daliban na bukatar Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa, yayin da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi watsi da bukatar da ma yiwuwar tattaunawa da ’yan bindigar.

Wata daliba a yayin zanga-zanga

Iyayen yaran sun bayyana damuwarsu kan abin da suka kira halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna tun bayan sace ’ya’yan nasu tsawon mako guda.

Dalibai da iyayen sun rikga daga kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce ‘Kawo karshen garkuwa da daliban FCFM’, inda suka yi tattaki tun daga sabuwar hanyar Mando zuwa tashar jirgin kasa da ke Rigasa, a Kaduna.

Daya daga cikin iyayen daliban da aka sace, Sunday Musa, ya ce ba za su iya ci gaba da jitran gawon shanu ba, don haka ne suka shirya zanga-zangar.

A ranar Juma’a masu garkuwa da daliban suka yi amfani da shafukan sada zumuntan wasu daga cikin daliban da ke hannunsu, wajen fitar da bidiyon da ke nuna halin da daliban ke ciki.

Daliban na rokon gwamnati ta taimaka da kubutar da su daga hannun maharan.