Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar ya haura daga 60 zuwa 75.
Kwamishinan Lafiyar Jihar, Yakubu Nuhu Danja ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin haske ranar Talata a birnin Dikko.
A cewarsa, adadin wadanda cutar ta harba ya karu daga 1,400 zuwa 1,534 a Kananan Hukumomi 25 da ke fadin jihar.
Danja ya yi bayanin cewa Karamar Hukumar Funtua tana da mutum 18 da suka mutu, Charanchi 14, Jibiya 11, Kankara 5, yayin da Sabuwa da Rimi suka samu mutuwar mutum hudu kowannensu.
Ya kara da cewa, an samu mace-macen ne a tsakanin 5 ga Mayu zuwa 8 ga Agusta, 2021.
“Jihar ta samu rahoton farko na wanda ake zargi da kamuwa da kwalara daga ranar 5 ga Mayu, 2021 a Funtua.
“Ya zuwa ranar 8 ga Agusta 2021, an samu jimillar mutane 1,534 da suka harbu kari a kan mutuwar 75 a Kananan Hukumomi 25.
“Alkaluman annobar sun nuna galibi wadanda suka kamu sun kai shekaru 15 zuwa sama kuma kashi 53 cikin dari maza ne.
Kwamishinan ya ce kalubalen tsaro na hana ma’aikatan kiwon lafiya samun damar shiga wasu yankuna don gudanar da binciken kan cutar.
Haka kuma, ya ce shigowar da wasu baki ke yi cikin jihar shi ma ya taimaka wajen barkewar cutar.
A kan haka ne ya ce an bullo da tsarin gano asalin wanda suka kamu da cutar kwalara a jihar don samun damar kawo karshenta.
Ya kara da cewa an raba kayan aiki da za su taimaka wajen yin gwaji cikin sauki, musamman a Kananan Hukumomi da cutar ta fi ta’azzara.