Ana fargabar cewa cutar Kwalara ta yi ajalin wasu mutum bakwai a garin Tella da ke Karamar Hukumar Gassol ta Jihar Taraba.
Aminiya ta ruwaito cewar cutar Kwalarar ta barke a yankin Kabawa a makon da ya gabata, kafin daga bisani ta yadu zuwa wasu sassa na garin.
- Sarakuna za su iya magance matsalar tsaro — Buratai
- Za a fara farautar masu tayar da zaune-tsaye a Jos
Wani mazaunin garin mai suna Mallam Ibrahim Halidu, ya shaida wa Aminiya cewar ya zuwa yanzu mutum bakwai sun rasu, sannan an kwantar da mutanen yankin da dama a asibitin gwamnati da ke garin.
Ya ce jami’an lafiya daga Hukumar Lafiya ta Karamar Hukumar Gassol sun ziyarci yankin Mutum-Biyu a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar.
Sai dai kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Gassol, Musa Chul ya ci tura.
Kazalika, Kwamishinan Lafiyar Jihar, Dokta Innocent Vakkai da wakilinmu ya tuntube shi, ya ce ya tuntube shi zuwa ranar Talata saboda a halin yanzu yana tsaka da ganawa da wasu baki na musamman.