✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci

’Yan bindiga ne suka kashe mahaifinmu bayan karɓar kuɗin fansa har Naira miliyan 9.

Wani basakkwace, Musa Abubakar, wanda a bayan nan ya yi ridda saboda zullumin ’yan bindiga masu kai hare-hare da ta’adar garkuwa da mutane, ya sake karɓar addinin Musulunci.

A ranar Asabar ce mutumin tare da matansa biyu suka sake karɓar addinin Islama bayan  ridda da suka yi a kwanan baya.

Bayanai sun ce Musa Abubakar ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Sakkwato ya yi ƙaura zuwa Jihar Taraba a sakamakon yanayin tsaro a mazauninsa.

Bayan komawa Taraba ne kuma ya shawarci matansa uku da su  karɓi addini Kiristanci, kuma ya yi nasara biyu suka amince.

Sai dai wannan lamari ya tayar da ƙura musamman a Sakkwato, inda har ta kai ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya haɗa kwamitin malamai domin su faɗakar da Musa kan ridda da ya yi.

Aminiya ta ruwaito cewa mambobin kwamitin sun haɗa da Alƙalin Alƙalai na Sakkwato, Malam Ahmad Umar Helele da Sarkin Malamai, Malam Yahya Na-Malam da kuma Malam Bashir Gidan Kanawa a matsayin sakataren kwamitin.

A yayin ganawa da mambobin kwamitin, Musa Abubakar ya shaida musu dalilan da suka fusata shi ya yi ridda ya koma Kirista.

Da yake zantawa da manema labarai kan binciken kwamitin, Malam Gidan Kanawa ya bayyana cewa, Musa Abubakar yana da ƙarancin ilimin addini baya ga rasa sana’arsa da ta’addancin ’yan bindiga ya haddasa.

“Wannan lamari ne ya fusata shi, ya jefa shi cikin ƙuncin rayuwa kuma ya yanke shawarar ƙaura zuwa Taraba, inda a nan aka yi amfani da tallafin kuɗi wajen kwaɗaita masa shiga Kiristanci,” in ji shi.

Da yake bayyana halin da shiga, Musa Abubakar ya ce ya yi ridda ne watanni kaɗan da suka gabata, amma a yanzu ya sake karɓar addinin Islama a sakamakon faɗin tashin da ’yan uwansa da malamai da shugabanni suka yi.

“A yanzu na dawo na karɓi addina na Islama tare da iyalina. Na yi nadamar abin da na aikata da kuma damuwar da na jefa ’yan uwa da malamai.

“Yamzu ga ni na dawo Sakkwato kuma zan ci gaba da sana’a da sauran harkokin kasuwanci,” in ji Musa. Ya sha alwashin cewa shi da iyalansa za su sadaukar da rayuwarsu a kan addinin Islama. A nasa jawabin, wani yayan Musa Abubakar, Alhaji Adamu Sabon Birni, ya ce “ta’addancin ’yan bindiga masu garkuwa da mutane ne ya yi ajalin mahaifina.

“’Yan bindiga ne suka kashe shi bayan karɓa kuɗin fansa har Naira miliyan 9 amma hakan bai sa na yi ridda ba, saboda matsalar ta’addancin ’yan bindiga ba iya Sakkwato kaɗai ake fama da ita ba.

“A duk faɗin Arewa ana fuskantar wannan matsala kuma mahukunta na iya ƙoƙarinsu wajen magance ta.

“Saboda haka a yanzu muna farin ciki ya gane kuskuren da ya yi kuma ya sake karɓar addinin Musulunci.

Matan Musa Abubakar da aka zanta da su sun ce za su iya ƙoƙari wajen goyon bayan mijinsu don ganin ya ci gaba da zama a Sakkwato kuma ya dawwama a kan tafarkin addinin Islama.