✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 11, ta kwantar da 200 a Taraba

Cutar ta mamaye kauyuka da ma a Kananan Hukumomin Bali da Gashaka

Mutum 11 ne suka mutu, yayin da 200 ke kwance a Babban Asibitin Bali da Serti da ke  Jihar Taraba, sakamakon bullar cutar Kwalara a kananan hukumomin Bali da Gashaka.

Aminiya ta gano cewa kauyen Takalafiya da ke karamar hukumar Bali ya fi kowanne yawan wadanda suka harbu da cutar, kuma daga nan ne kuma cutar ta yadu zuwa yankunan birnin Balin da wani bangare na Karamar Hukumar Gashaka.

Mazauna yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa annobar Kwalarar ta bulla ne a makon da ya gabata, kuma ta mamaye kauyuka da dama a kananan hukumomin biyu.

Wani mazaunin yankin, Bello Dauda, ya ce yawanci wadanda suka mutu sanadiyar amai da gudawar sun fito ne daga kauyen Takalafiya inda cutar ta fara bulla.

Tawagar jami’an lafiya daga ma’aikatar lafiya na ta kokarin shawo kan annobar da kuma wayar da kan al’ummomin yankin kan matakan kariya domin dakile cutar.

Yunkurin ji ta bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar Taraba, Dokta Innocent Vakkai, ya ci tura, domin ya ki amsa waya ko daukar sakonnin da muka tura mishi.

Idan za a iya tunawa, a watan jiya ne hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa ta ce cutar ta kashe akalla mutum 31 a jihohin kasar nan 15, kuma jihar ta Taraba da Kurso Riba ne ke da rinjayen wadanda suka kamu.