Darakta-Janar na Cibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Jide Idris, ya ce an samu mutane 2,102 sun kamu da cutar amai da gudawa ta kwalara.
Ya bayyana cewa cutar ta yi ajalin mutane 63 a jihohi 33 da ƙananan hukumomi 122 tun daga farkon shekarar nan zuwa 30 ga watan Yunin 2024.
- Ya shiga hannu kan damfarar mahajjata Naira miliyan 4.5
- Gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyin Ilimi ba — Minista
Idris ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ya kara da cewa adadin waɗanda suka mutu a sakamakon cutar ya kai kashi uku cikin 100 na wadanda suka kamu da ita.
Ya ci gaba da cewa, jihohi bakwai daga cikin 10 na farko sun ne Legas, Bayelsa, Abiya, Zamfara, Bauchi, Katsina, Cross Riɓer, Ebonyi, Ribas da Delta.
Jihohin da ke dauke da kimanin kashi 90 cikin 100 na masu fama da cutar kuma jihohin Kudu ne.
Kwalara, cuta ce mai saurin yaɗuwa a abinci da ruwa, wadda a baya-bayan nan ta tada hankula a jihohi da dama a Najeriya.
Tana faruwa ne ta hanyar shigar ƙwayoyin halitta vibrio cholerae cikin gurbataccen ruwa da abinci.
Ya ce, “Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kwalara ta Ƙasa ta sanya ƙwararru domin yaki da cutar tare da bayar da rahotannin yanayi na lokaci zuwa lokaci ga masu ruwa da tsaki.
“Haka zalika wannan yana tabbatar da ingantaccen haɗin kai, da daidaito a rabon kayan agaji don tallafa wa jihohin da abin ya shafa,” in ji shi.