Jami’an Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kwara, ta kama wani mutum mai suna Ganiyu Yusuf Olalekan kan zargin damfarar Mista Ibrahim Mustapha da wasu mutum biyu kuɗi Naira miliyan 4.5.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya yi ƙaryar cewa shi ɗan siyasa ne, kuma babban ma’aikaci a Ma’aikatar Kuɗi tare da yi wa wanda abin ya shafa alƙawarin aikin Hajji guda uku a madadinsa.
“Bayan yin bincike, an gano cewa wanda ake zargin ɗan damfara ne da ke yaudarar jama’a da ba su ji, ba su gani ba, don neman kuɗi,” a cewar sakataren yaɗa labaran NSCDC, Ayoola Michael.
Ya ƙara da cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargi da laifin yin sata a cikin gida.
Ya ce, jami’an rundunar sun gano wani Ibrahim Wasiu mai shekara 31, mazaunin garin Eyenkorin, bayan wani rahoto da wani mai suna Mumini Kabir ya bayar game da wasu ɓarayin da suka fasa gidansa.
A cewar mutumin, sun wawushe wasu kayayyaki masu daraja da suka haɗa da babur, wayoyi ƙirar Android guda biyu, na’urar sauti ta gida da dai sauransu.
“A ranar 30 ga watan Yuni, 2024, an gano wani wanda ake zargi, mai suna Soliu Jimoh, mai shekara 33, kuma an kama shi da laifin satar igiyoyin lantarki da kayan aiki na gine-ginen da ake ginawa a Gaa Ajanaku, a yankin Ilorin,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, an ƙwato dukkanin kayayyakin da aka sace da suka haɗa da wayoyi da kayan aiki.
“Dukkan waɗanda ake zargin sun amsa laifin da suka aikata kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.”