Tambari
Turnukun tarar tattare tari
Tarnakin tokari
Taga-tagar tattagar turi
Turun takalar ja-in-jar jinkiri
Kwakwa-kwakwa
Agwawa-agwagwa
Gumurzun gwagwa-gwagwa
Kwakwar kwakumar kanwa
Kukin kanwar kawa
Kulunboto
Kullin kululu katoto
Kokarin kankame koto
Kasurar kasaitar kankantar kato
Kulafucin karantar tauna toto
Kurungun babba mai rawani
Asusun alkinta awalaja
Takun sakar jayayya gaja-gaja
Masu tara haraji na basaja
Harkar dai tai ta rudani
Gangin gidan waya
Garar garangadin garaya
Gargarar gangarar gingiya
Gadarar gada-gadar gogayya
Gigiwar giwayen gayya-gayya
Hatimin hakimi
Samamen some-somen masomi
Hakilon mai makami
Mamungar murkushe mukami
Kwanjin karin kaimi
Janjamin jimami
Likon lakabin limami
Kundunbalar karfafa kumewar kumaji
Zullon zalamar zullumi
Gararumar galala galmi-galmi
Hakika daf da karkarewar shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa, an yi takaddamar tataburzar turka-turkar takun-sakar Kwakwar kwakumar kawanyar kurungun kasaita, a tsakanin Hukumar Gidan Waya da Hukumar Harhada Harajin Hadakar Haurobiya. Shin ko gwamnati ta girgije ta gyagije gunjin gumurzun?
Har yanzu dai babu wani batun bututun bayyanai. Sai dai sanin kowa ne cewa, tambarin kurungun babban mutum mai kambin jan ragamar al’umma a gargajiyance ya fi kawo wa gwamnatin dimbin matsabbai fiye da zamanin da kawai ake likawa don aikewa da sakonnin watsattsaken wasiku. Tunda a halin yanzu daukacin Asusu-asusun alkinta awalaja da ke fadin Haurobiya an shardanta musu wajibcin biyan ’yan matsabban lika tambarin kambin jan ragamar al’umma da kimar darajarsa ta kai Hauro babban lauje da zagaye ba wani zagaye-zagaye.
Wannan jimurdar janjanin ja-in-ja ta haifar da tunkarar tambarin turnukun tarar tattare tarin tarnakin tokarin taga-tagar tattagar turin
turun takalar ja-in-jar jinkiri, ana ta kugin kwakwa-kwakwa agwawa-agwagwa da ke ta gumurzun gwagwa-gwagwar kwakwar kwakumar kawa-zucin kukin kanwar kawa. Sai aka zo ana ta kulunboton kullin kululun katoton kokarin kankame koton kasurar kasaitar kankantar katon kulafucin karantar tauna toto
Shi dai kurungun babba mai rawani ko kambin jan ragamar al’umma da ake likawa a watsattsaken wasiku, yanzu ya zamo tambarin tabbatar da ingancin hada-hadar asusu-asusun alkinta awalaja. Wannan lamari dai ya haifar da takun sakar jayayya gaja-gaja a tsakanin masu tara haraji da ke ta harin jajin basaja, har ta kai ga harkar na ta yada rudani.
Gurmin gangunan gangin gidan waya da garar garangadin garandi-garandin garayar gargarar gingimemiyar gingiyar gadarar gada-gadar gogayyar gigiwar giwayen gayya-gayya. Don hada-hadar handame Hatimin hakimin samamen some-somen masomin hakilon mai makamin mamungar murkushe mukamin mamuke kwanjin karajin karin kaimi.
Hakika ina da masaniyar cewa, masu falle falle-fallen jirwayen jerin jaridu da makalutun makalolin mujallu, tare da masu baje na-zomo a akwakun kwakwazo da wulkita na-mujiya a akwatunan dodannin hotuna masu wuntsila gudi-gudi, ka iya bijiro mini da tambaya kan takaddamar gidan waya da hukumar harhada harajin Haurobiya; ko ma wasu su furta cewa, don mene ne a farfajiyar makarantar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar kasar Haurobiya za a yi waiwayen watayawar wulkice-wulkicen batutuwan shekarar da ta rare ta arce a guje?
Hujjata dai ba ta wuce karamin lauje ba, wato da farin farawa dai shi ne lamirin lamarin janjamin jimamin likon lakabin limamin kundunbalar karfafa kumewar kumajin zullon zabarin zalamar zullumin gararumar garar galalar galmi-galmi. Kun ga ke nan matukar mahukunta ba su warware wannan wuni-wunin ba, to akwai yiwuwar a yi wa hukumar gidan waya wa-ka-ci-ka-tashi, shi ke nan, wai Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan-sa ba tare da sa-in-sa ba, ya ce “kura da shan jibga, gardin garada da cafke matsabbai.”
Daddale dalili na karamin lauje, shi ne, na baje na-zomo, inda na yi kasake ina sauraren Babban bakin ce-ce-ku-cen Birtaniyawan birnin Lantsandan, inda aka tabbatar mini sun yi hadin gwiwar gwagwiyar goriba da MARKAZUZU ko MAKATAR-ZUR ko MAKE-ZUR, wato a shirin TANTANCE TSAKANIN TSABA DA TSAKUWA, inda za a bankado alkawurran da masu mamuke da madafun ikon wasan Samson-siyar dama-damar kurda-kurdar siyasa suka tsaya wajen cika-cikin cika alkawura cif-cif. Ni kuwa sai na ce ai ba wannan ma za a yi ba, a dai duba takaddamar da ke tsakanin sassan hukuma, wadanda ba sa ga-maciji da juna, ta yadda za a shawo kan lamarin kafin ya yi kamari.
Irin wannan turka-turka idan ta taso ko shigifar shari’a za a kai sassan da ke arangamar karon-batta da juna ko kuwa kundin kunshe tushe za a bincika a gano inda bakin azargagiyar zaren ta zurare? Matukar dai ba a yi mai yiwuwa ba, ai sai mu ce har yanzu mahukuntan kasar nan na fama da LAULAYIN ALAYEN LAUYE-LAUYEN DUKAN DOKOKI. Ko dai dokokin durfafar daki-dakin dakon dakon al’amuran kasa na fama da farmakin TASGARON TUMADUGAYYA ne?
“Kai mutan gidan ga ku taya ni dibi, dan ga sai boda shi kai, shina kari, ko tarmanina ya cije shi,” a cewar wata gyatuma ’yar birnin Shehu Mujadaddi. Ni kuwa na so in ce ai iya sai kiyi “na damo,” domin cinnaka bai san na gida ba.
Lallai Gwamnatin Baban-burin-huriyya ta hanzarta ta yi wa tufkar hanci, don ka da a jefa ’yan kwadago cikin kunci, musamman ma ganin yadda aka lakume lomar lamarin kare-karen kadagon kunduge kokon koto.