✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwadon rama ya yi sanadin rasuwar daukacin iyali

Wani Sufeton ’yan sandan kwantar da tarzoma da matarsa mai juna biyu da ’ya’yansu biyu namiji da mace sun gamu da ajalinsu a kauyen Dusai…

Wani Sufeton ’yan sandan kwantar da tarzoma da matarsa mai juna biyu da ’ya’yansu biyu namiji da mace sun gamu da ajalinsu a kauyen Dusai da ke masarautar Kagoro a karamar Hukumar kaura da ke Jihar Kaduna bayan cin ganyen rama.

Marigayin mai suna Peter Dauda, dan shekara 45, dan sandan kwantar da tarzoma ne da bai dade da kaiwa matsayin sufeto ba, sai matarsa Dorathy Dauda mai dauke da juna biyu da kuma ’ya’yansu Godwin Peter dan shekara tara da Patience Peter ’yar shekara shida.

kanen marigayin mai suna Elkana Dauda ya shaida wa Aminiya bayan ta ziyarci gidan, cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis din makon jiya bayan sun ci ganyen ramar da ta kai mako guda a shanye. “Da ni aka ci ramar a ranar farko bayan an kwadanta kuma babu abin da ya same mu duka a lokacin. Bayan nan ne suka shanya ragowar ramar a saman rufi, ni kuma a wancan ranar na tafi Abuja. To bayan mako guda ramar tana shanye da Alhamis ta kewayo suka tafi gona suka dawo a gajiye, kuma ba su dawo gida da wuri ba, sai suka ce bari su kwadanta saurar ramar da suka shanya ba sai sun yi wani girki ba,” inji shi.

Ya ce “Bayan cin ramar, washegari Juma’a sai karamar ’yarsu Patience mai shekara shida ta rasu da yamma kuma sai namijin Godwin mai shekara tara ya bi ta, daga nan ne aka garzaya da iyayen zuwa Babban Asibitin Kafanchan, inda washegari Asabar da safe mahaifiyar yaran da take dauke da tsohon ciki ta rasu. Daga nan ne aka buga min waya na taso daga Abuja na zarce asibitin Kafanchan inda na tarar da dan uwana kwance ana kara masa ruwa.”

Elkana ya ci gaba da shaida wa Aminiya cewa daga nan ne ya karbi wani kanensu da ya kwana da shi suka ci gaba da hira da shi yana daga kwance. “Zuwa can sai ya ce min yana jin bayan gida na raka shi zuwa bayi, amma ya kasa yin ba-hayar, haka muka dawo daki zuwa can kuma sai ya ce min yana jin zafi a jikinsa yana so a fitar da shi waje domin ya sha iska, shi ne na tambayi masu kula da shi suka ce ba damuwa muna iya fitar da shi, to sai na ga hakan ma wata wahala ce bari na garzaya kawai in dauko masa fanka shi ne na tafi Unguwar Garaje na dauko masa fanka ban fi minti biyar da dawowa ba sai shi ma ya cika,” inji shi.

Ya bayyana cewa a yanzu babu wanda suke zargi domin marigayin ba ya da abokin fada, amma sun tabbatar cewa guba ne aka zuba musu a ramar kamar yadda aka tabbatar musu a asibiti, sai dai ba su san wa ya sa gubar ba kuma ba su zargin kowa don haka sun barwa Allah komai.

Wata majiya daga cikin gidan marigayin da ta shaida wa Aminiya cewa wannan lamarin guba ne aka sanya musu domin mako biyu kafin faruwar lamarin an sanya wa dabbobinsa guba inda suka mutu.

Aminiya ta tuntubi mahaifiyar marigayin mai suna Monica Dauda mai kimanin shekara 65 inda ta kasa cewa komai saboda jimamin abin da ya faru da danta inda tashi daya babu shi babu zuriyarsa, domin

jaririnsu ma ya rasu ne a bara.

Shugaban riko na karamar Hukumar kaura da Sarkin Kagoro da Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Mista Barnabas Bala Banted sun kai wa dangin mamatan ziyarar ta’aziyya da jaje.