Dakarun sojojin Najeriya na Operation Haɗin Kai da rundunar sojin sama sun daƙile wani harin haɗin gwiwa da ‘yan ta’addar ISWAP suka kai a garin Damboa, inda suka kashe mahara 16 a wani ƙazamin faɗa da suka yi cikin dare.
Mai sharhi kan lamarin tsaro Zagazola Makama ya samu labarin cewa, harin ya afku ne a ranar Juma’a, inda aka kai harin da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare da wayewar garin ’yan tada ƙayar bayan sun kai hari a kan gadar Azir da kuma runduna ta 25 da ke Damboa.
- An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya
- 2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa
Majiyoyin sun ce dakarun da ke samun goyon bayan jiragen sama daga rundunar sojin sama, sun yi ta artabu da ’yan ta’addan a wani farmakin da ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu ana yi.
“Babban abin da ’yan ta’addan suka sa a gaba shi ne murƙushe birget ɗin soja da ke Damboa, inda suka kai hari ga jama’a, sai dai sojojin sun mayar da martani da ƙarfin wuta, wanda ya yi sanadin jikkatar ‘yan ta’addan da dama,” in ji ɗaya daga cikin majiyoyin.
“Aƙalla gawarwakin ’yan ta’addan 16 ne aka tsinto bayan musayar wuta da aka yi, wasu da dama kuma da ake kyautata zaton sun gudu da raunukan harbin bindiga, sai dai abin takaicin shi ne, sojoji biyu sun rasa ransu a lokacin fafatawar da ’yan ta’addan.
Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa yayin da sojojin suka samu nasarar shawo kan lamarin, fashewar ɗaya daga cikin nakiyoyin ’yan ta’addan ya haddasa gobara a wani wurin ajiyar alburusai, wanda ya yi tasiri ga gine-gine biyu wanda nan take aka shawo kan gobarar.
A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan zaƙulo ‘yan ta’addan da ke tserewa, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto a kewayen yankin baki ɗaya.
Garin Damboa da ke kudancin Borno, ya sha fuskantar hare-haren ISWAP a lokuta da dama, saboda kyakkyawan wurin da yake.
Sai dai rundunar sojin Najeriyar na ci gaba da fafatawa a yankin domin hana faɗawa hannun ’yan tada ƙayar baya.
Rundunar sojin Operation Haɗin Kai da ke yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ta ƙara ƙaimi a ’yan makonnin nan, inda ta samu gagarumar nasara a kan mayaƙan ISWAP da ’yan Boko Haram a jihohin Borno da Yobe.