✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kurtu ya yi tatul da giya ya kashe Birgediya Janar a bariki

Da farko mun hango wannan Soja cikin motarsa a guje yana ta tangal-tangal ya wuce mu.

Wani kurtu da tuni na tsare a hannun rundunar sojin kasa ya kashe Birgediya Janar O.A. James a barikin sojoji da ke Abuja ranar Talata.

Premium Times ta ruwaito majiyar na cewa, wannan kurtu dai ya fito ne daga gidan giya bayan ya yi mankas dinsa.

Majiyar ta ce bayan fitowarsa ce ya shiga motarsa ya rika tangale-tangale da ita a bariki a yayin da Janar James ke tafiyarsa a kafa salin-alin za shi gidansa da ke cikin bariki.

“Da farko mun hango wannan Soja cikin motarsa a guje yana ta tangal-tangal ya wuce mu, daga nan ne muka ji kwatsam ya daki wani abu.

“Ashe Birgediya Janar James ne ya buge. Ko da aka garzaya da shi zuwa asibiti, likitoci nan take suka ce ya rasu.

Rundunar Sojoji ta tsare wannan kurtu zuwa a kammala bincike a kan abinda ya faru.

Janar James, babban soja ne da ke aiki a sashen kudi na rundunar Sojin Najeriya.